Rikicin PDP: Shugaban Jam'iyya Ya Aike da Sabon Gargadi

Rikicin PDP: Shugaban Jam'iyya Ya Aike da Sabon Gargadi

  • Ambasada Umar Iliya Damagum ya yi magana kan rikicin da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ke fama da shi
  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, ya gargaɗi masu amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya a kan jam'iyyar
  • Damagum ya buƙaci shugabanni da mambobin PDP da su ba da fifiko wajen haɗin kan jam'iyyar maimakon kawo rarrabuwar kawuna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya ja kunnen masu ƙoƙarin kawo rikici a jam'iyyar.

Umar Damagum ya gargaɗi masu amfani da kafafen sada zumunta kan gujewa yaɗa bayanan ƙarya da za su iya kawo cikas ga jam’iyyar.

Shugaban PDP ya aika da gargadi
Umar Damagum ya ja kunnen masu amfani da kafafen sada zumunta Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce shugaban na PDP ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ƙarshen taron ƙarawa juna sani na kwanaki biyu kan wayar da kai a fannin yaɗa labarai ga masu amfani da kafafen sada zumunta a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi fallasa, ya zargi ciyamomi da turawa shugabannin PDP N12bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban PDP ya yi gargadi

Damagum ya jaddada cewa jam’iyyar PDP ta fi ƙarfin kowane mutum, kuma rikice-rikicen cikin gida ba za su iya kawo ƙarshenta ba.

Shugaban na PDP wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Hon. Yusuf Dingyadi, ya yi kira ga mahalarta taron da su fifita yaɗa manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar.

Ya jaddada muhimmancin ɗa’a da hadin kai a cikin jam’iyyar, tare da yin Allah-wadai da masu amfani da rikice-rikicen cikin gida don yaɗa ƙiyayya da rarrabuwar kawuna, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Damagum ya bayyana ƙudirinsa na tabbatar da yafiya, zaman lafiya, da haɗin kai a cikin jam’iyyar, yana mai cewa ba za a lamunci rashin adalci ko yaɗa farfaganda a ƙarƙashin shugabancinsa ba.

Wace shawara Damagum ya ba da?

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da mambobinta da su guji yin abubuwan da za su ɓata sunan PDP.

Kara karanta wannan

Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan masu yi wa kasa hidima N77,000

"Ɓangarorin jam’iyyar mu, musamman kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) a ƙarƙashina, sun duƙufa wajen nemo mafita ga ci gabanmu maimakon rura wutar rikici."
"Ruruta rikice-rikicen cikin gida da fifita son kai a kan haɗin kan jam’iyya yana da illa ga abin da shugabanninmu na farko suka gina PDP a kai."

- Umar Iliya Damagum

Shugaban PDP ya ba da tabbaci

Damagum ya kuma tabbatarwa mambobin jam’iyyar da cewa ya ƙudiri aniyar tabbatar da haɗin kai, ɗa’a da ci gaba a matsayin ginshiƙin shugabancinsa.

Ya kara da cewa PDP za ta ci gaba da zama da ƙarfinta, tare da yin kira ga dukkan mambobin da su fifita muradun jam’iyya a kan bukatun kansu domin tabbatar da ci gabanta.

PDP ta hango nasara a zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar, ya yi magana kan makomar PDP a zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi magana kan gwamnan da ake tsoron zai sauya sheka zuwa APC

Kwamitin na NWC ya bayyana cewa jam'iyyar PDP za ta samu ƙarin gwamnoni a 2027 domin ƴan Najeriya sun gaji da APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng