Ministan Buhari Ya Tona Irin Mutane Masu Hadarin da Suka Kewaye Bola Tinubu
- Solomon Dalung ya bayyana cewa 'yan-ba-ni-na-iya da ke kusa da shugaba Bola Tinubu sun fi na Muhammadu Buhari karfi da hatsari
- Tsohon ministan ya ce 'yan-ba-ni-na-iyan Tinubu na da ilimi mai zurfi da fahimtar yadda ake sarrafa mulki da kawar da hankalin gwamnati
- Solomon Dalung ya bayyana cewa mutanen za su iya yin illa ga mulkin Bola Tinubu tare da jefa ‘yan Najeriya cikin damuwa da talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa 'yan-ba-ni-na-iya da ke kusa da Bola Tinubu su fi na gwamnatin Muhammadu Buhari dabara.
Solomon Dalung ya yi zargin cewa 'yan-ba-ni-na-iyan na amfani da kwarewarsu wajen hana samun sahihan bayanai da kuma ware Tinubu daga samun cikakken ikon tafiyar da mulki.
Dalung ya yi wannan furucin ne a wani shiri na gidan talabijin din Channels a ranar Talata da aka tattauna batutuwan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Solomon Dalung ya ce wasu na juya Bola Tinubu
Solomon Dalung ya bayyana cewa 'yan-ba-ni-na-iya a lokacin gwamnatin Buhari ba su da cikakken ilimi ko kwarewa wajen tafiyar da mulki.
“'Yan-ba-ni-na-iya a gwamnatin Buhari mutane ne da ba su da cikakken fahimta game da siyasa, mulki, da gudanar da al’amuran gwamnati.
"Ayyukansu sun takaitu ga ra’ayoyin kansu da biyan bukatun kansu ne kawai”
- Solomon Dalung
Amma ya ce 'yan-ba-ni-na-iyan Tinubu na kunshe da mutane masu ilimi, tsari, da fahimtar dabarun mulki, wanda hakan ke sa su fi tasiri da hatsari.
Barista Dalung ya kara da cewa sun fi kwarewa wajen yin amfani da mulki, boye bayanai da kuma toshe wasu kofofi ga shugaban kasa.
Dalung: Tinubu na cika alkawari ga talakawa?
Solomon Dalung ya ce zai kasance rashin adalci ga ‘yan baya a musanta samuwar 'yan-ba-ni-na-iya da ke amfani da mulki wajen cika muradun kansu ba tare da kula da jama’a ba.
Tsohon ministan yana ganin cewa samuwar 'yan-ba-ni-na-iya ne ke hana shugaban kasa cika alkaruwaran da ya dauka.
A karkashin haka ya yi tambaya ko gwamnatin Tinubu na cika alkawarin da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ke cewa babbar bukata ita ce inganta jin dadin al’umma.
“Shin ‘yan Najeriya suna jin dadin manufofin wannan gwamnati? Tabbas ba haka ba ne. Talakawa suna cikin damuwa kuma ba su jin dadin abin da ke faruwa a mulkin nan.”
- Solomon Dalung
Dalung ya fadi matsalar da za a fuskanta
Solomon Dalung ya yi gargadi cewa tasirin 'yan-ba-ni-na-iyan Tinubu na iya yin illa ga shugabanci da jefa talakawa cikin mawuyacin hali.
Punch ta rahoto cewa Dalung ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su duba halin da ake ciki tare da tabbatar da cewa gwamnati ta koma kan turbar da za ta ciyar da kasar gaba.
An damka mulkin Ghana ga shugaba Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasan Ghana ya yi kuskure, har ya mika mulki ga Bola Tinubu yayin da aka rantsar da shi.
Shugaba John Mahama ya yi kuskuren kiran Bola Tinubu da shugaban Ghana, lamarin da ya jefa al'umma da dama cikin mamaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng