Jagora a Kwankwasiyya Ya Fadi Abin da Ya Hana Manyan NNPP Komawa APC a Kano
- Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa akwai rikici mai tsanani a jam’iyyar APC a Kano, wanda ya zarce na cikin NNPP
- Ya ce kan APC a Kano a rarraba yake, kuma rikicin ya samo asali ne daga kulle-kullen da ake yi domin ganin an tumbuke Ganduje
- Hon. Kofa mai wakiltar Kiru da Bebeji ya nanata cecwa rikicin APC na daga cikin abin da ya hana wasu 'yan NNPP sauya-sheka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jagora a NNPP kuma Dan Majalisar Wakilai, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan jam’iyyarsa ba za su koma APC mai mulki ba saboda wasu dalilai.
Ya bayyana cewa akwai manyan rigingimun da ke kunshe a cikin jam’iyyar APC a Kano ya na daga cikin abubuwan da ke takawa ‘yan NNPP da ake zaton za su bar jam’iyyar birki.
A wata hira da ya yi da Freedom radio da aka wallafa a shafin Facebook, Hon Kofa ya bayyana cewa kan APC a Kano a rarraba take, kuma Ganduje ne uwa da makarbiyarta a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa akwai babban dalilin da ya sa wadanda ake zargi da son barin NNPP suka saurara, inda ya ce har yanzu ba su fito sun bayyana ficewa daga jam’iyyarsu ba.
“Akwai rigingimu a jam'iyyar APC,” Kofa
Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya shaida cewa ya na kyakkawar alaka da wasu daga cikin ‘yan APC a Kano, kuma ya san kulle-kullen da ake yi wajen ganin an kawar da shugabancin Ganduje a matakin kasa.
Hon. Kofa ya kara da cewa
“Duk wannan kulle-kullen da ka ke gani ake ta yi, a’a, za a kori Ganduje a shugaban jam’iyya na kasa da sauransu, Wallahi Tallahi ta na da tushe daga Kano.”
“Akwai manya-manyan ‘yan APC a Kano, ni ina gaya maka abin da na sani, na san Abuja kamar tafin hannuna.
"Duk inda suka shiga suka yi magana, na sani. Wallahi Tallahi su suke kulla masa wannan abin. Ka ce wai Ganduje bai sani ba?”
Kofa: Ganduje yana kulle da ‘yan APC
'Dan majalisar tarayyar mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya na fakon wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar.
“Ya na kallonsu, zai taho da gudumarsa, duk ya fi su sanin siyasa. Ai magana na ke na nuna maka cewa, rigimar da ke cikin APC, ta fi ta NNPP.
Hon. AbdulMumin Kofa ya kara da cewa duk wanda ya fice daga NNPP zuwa APC ya jefa cikinsa a wuta saboda mummunan rigimar da ta ke fama da shi.
Ya kara da cewa har yanzu, NNPP ta na maganar a zauna a hade guri guda, saboda haka maganar sauya jam’iyya zuwa APC kamar yi wa kai mummunan makomar siyasa.
'Yan NNPP da ake zargin komawarsu APC
Duk da Hon. Kofa bai kama suna ba, amma ana zargin 'yan majalisun Kano guda biyu da su ka bayyana ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya ne za su bar NNPP.
Aliyu Sani Madakin Gini (Dala) da Alhassan Rurum (Rano/Kibiya/Bunkure) sun barranta kansu da tafiyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso saboda wasu dalilai.
Kofa ya janye goyon bayan kudirin APC
A baya kun ji Dan Majalisa mai wakiltar Kiru/Bebeji, AbdulMumin Jibrin Kofa ya nemi afuwar 'yan mazabarsa da sauran jama'ar Arewa bisa goyon bayan kudirin haraji.
Hon. Kofa, ya na daya daga cikin 'yan adawa da su rika nuna goyon baya ga kudirin harajin da al'umma da shugabanninsu ke ganin zai jawo wa yankin koma baya idan ya tabbata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng