Jagora a APC Ya Tube Ganduje, Ya Bayyana Masu Taimakon Jam'iyya da Gaske

Jagora a APC Ya Tube Ganduje, Ya Bayyana Masu Taimakon Jam'iyya da Gaske

  • AbdulMajid Mustapha Kwamanda ya zargi shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da yaudarar Mataimakin Shugaban kasa
  • Kwamanda, wanda jigo ne a APC ya bayyana cewa Abdullahi Ganduje na tsoron hadin kai da Shettima saboda fargabar rasa kujerarsa
  • Dan Bilki ya zargi Ganduje da watsi da 'yan APC a Kano, yana mai cewa suna bin tsirarun 'yan jam'iyya da ake ganin suna da kayan aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Guda daga cikin 'yan jam'iyyar APC a Kano, AbdulMajid Mustpha Kwamanda ya zargi shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da yaudarar Kashim Shettima.

Ya bayyana cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mukarrabansa ba sa kaunar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, shi ya sa ake taka tsan-tsan wajen nuna goyon baya.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: Abba ya hana ni zuwa aikin hajji duk da taimakon Kashim Shettima

Ganduje
Dan Bilki ya zargi Ganduje da cin dunduniyar jam'iyya Hoto: Kashim Shettima/AbdulMajeed Mustapha Kwamanda/Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwamanda ya zargi Abdullahi Ganduje da manufunci irin na siyasa, kuma ya zama annoba ga tafiyar APC kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kware wajen hada makircin siyasa, wanda shi ya sa ya ke samun wasu damammaki a tafiyar siyasarsa.

Ana zargin Ganduje da kin Shettima

Jigo a APC, AbdulMajid Kwamanda ya bayyana dalilin da ya sa ya ke zargin Abdullahi Umar Ganduje ke tsoron tafiya tare da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Ya bayyana cewa Abdullahi Umar Ganduje ya na kin aiki tare da Sanata Shettima ne domin farganbar rasa kujerarsa ta shugabancin APC a matakin kasa.

Ya ce;

"Wai abin da ya sa ba sa so su rakabe shi, saboda ana zargin takun-saka tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Saboda haka kar a gansu sun zo wajen, in ya so a zo aje a sutale Ganduje.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

"Ba ka ga yanzu munafuncin siyasar Ganduje da ya ji zai zo, ai Landan ya gudu, daga can ya wuce Umara. Duk shiri ne.

Ya jaddada cewa Abdullahi Ganduje ya na da masaniyar Mataimakin Shugaban kasa zai zo Kano, amma Ganduje ya sa kafa ya bar gari saboda kar ya tarbe shi.

An zargi Ganduje da makircin siyasa

Kusan na APC ya bayyana fargabar yadda Shugaban Jam'iyya na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kware a munafurci irin na siyasa.

"Shi kuma Kashim ya na ganin ya zo don ya habaka jam'iyya. A'a su ba sa son habaka jam'iyya.

Ya bayyana cewa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da Abdullahi Umar Ganduje annoba ce a jam'iyyar, kuma ba za su bari jam'iyyar ta yi nasara a zabe mai zuwa ba.

Kwamanda ya zargi Ganduje da watsi da APC

Kwamanda ya zargi Abdullahi Umar Ganduje da watsi da 'yan APC a jihar Kano, inda suka rike wasu sababbin 'yara' masu 'kayan aiki,' a maimakon ci gaban jam'iyyar.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

"Mutum uku su ka rike jami'iyya, akwai zababbe guda daya, Kabiru Abubakar Kabiru, Injiniya na Bichi, ya rike jam'iyya, ya rike 'yan Jam'iyya.
"A Sanata kuma, Maliya. Barau Jibrin ya rike jam'iyya. A kuma wadanda suka rasa mukami na jiha, suke taimakon matasa, babu irin Murtala Sule Garo.

Ya jaddada cewa Murtala Sule Garo ya na taka muhimmiyar rawa wajen rike matasan jam'iyya da sauran masoyan APC duk da bai da mukami.

Kwamanda ya gargadi Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa AbdulMajid Danbilki Kwamanda, jigo a APC na Kano, ya bayyana zargin cewa shugabancin Abdullahi Umar Ganduje da Abdullahi Abbas ya zama annoba garesu.

Kwamanda ya yi alkawarin jagorancin matasa don adawa da wannan shugabanci, yana mai cewa za su hargitsa jam'iyyar, inda ya kara da zargin Ganduje da watsi da bukatun 'yan APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.