Rikici da Gwamna Ya Jawo An Tsige Shugabannin Kananan Hukumomi daga Muƙamansu

Rikici da Gwamna Ya Jawo An Tsige Shugabannin Kananan Hukumomi daga Muƙamansu

  • Kasuwar tsige ciyamomin kananan hukumomi a jihar Edo na ci gaba da ci yayin da ƴan majalisar kansiloli suka kara tsige mutane
  • Ƴan majalisar sun sauke shugaban ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas da takwaransa na ƙaramar hukumar Akoko-Ado
  • Sai dai tsigaggun ciyamomin sun ce matakin da aka ɗauka a kansu ba zai je ko ina ba domin ya saɓawa tanadin dokar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Rikicin siyasa tsakanin gwamnatin jihar Edo karkashin Gwamna Monday Okpebholo da shugbaannin ƙananan hukumomi ya kara tsananta.

Ƴan majalisar kansiloli sun tsige shugaban ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, Dr. Kelly Ehidiamen Inedegbor da na ƙaramar hukumar Akoko-Ado, Tajudeen Alade.

Taswirar jihar Edo.
Kansiloli sun tsige ƙarin shugabannin ƙananam hukumomi 2 a jihar Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa kansilolon sun tsige ciyamomin guda biyu tare da mataimakansu kuma ana zargin duk shirin gwamnatin Okpebholo ne.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi fallasa, ya zargi ciyamomi da turawa shugabannin PDP N12bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka nemi jin ta bakin shugabannin kananan hukumomin aka sauke daga muƙamansu, sun ce wannan tsigewar ba za ta je ko ina ba domin an saɓawa doka.

Yadda aka tsige ƙarin ciyamomi 2 a Edo

A Uromi, hedkwatar karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, duka kansilolin ne suka amince da tsige ciyaman bisa zargin rashin ɗa'a da karya dokar rantsuwa.

Matakin dai ta biyo bayan wata takarda da kansiloli biyu, Hon Shedrack Onoghemenosen na gunduma ta 11 da Hon Samuel Udawele na gunduma ta 2 suka gabatar.

Har ila yau bayan tsige ciyaman, Hon Ubomesisi ya kuma sanar da dakatar da kansiloli uku watau Hon. Sunday Ebosele, Hon. Smart Eboigbe, da Hon. Kingsley Osehon saboda dalilan da ba a bayyana ba.

A garin Igarra kuma, hedkwatar karamar hukumar Akoko-Edo, wasu kansiloli ne suka shirya zama wanda a ƙarshe suka sanar da tsige ciyaman da mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

Kansiloli sun karɓe ragamar shugabanci

Bayan haka kuma suka ɗora shugaban kansiloli, Hon Alabi Oshionogue a matsayin muƙaddashin ciyaman sannan suka naɗa sabon shugaban majalisa.

Bayan ya karbi ragamar shugabancin karamar hukumar, muƙaddashin ciyaman ya ce an kafa kwamitin da zai kwato duk wasu kadarorin gwamnati da suka bata.

Bugu da kari ya rusa dukkan nade-naden da tsohon ciyaman na ƙaramar hukumar, Hon Alade ya yi nan take, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Hon Kabiru Adjoto wanda ya shaida zaman da kansiloli suka tsige ciyaman a Akoko-Ado, ya ce ya gamsu da yadda lamarin ya gudana cikin lumana.

Shugaban karamar hukuma ya yi martani

Da yake mayar da martani, Alade ya ce matakin kansilolin na tsige shi ya saba doka, inda ya zargi masu son wawure dukiyar al'umma da kulla masa makirci.

“Abin da ake yaɗawa na batun sauke ni wasu tsirarun kansiloli ne suka aikata kuma ya sabawa doka. Kwanakin baya, wadannan mutanen suka shiga sakateriya suka kwashe mani kayana."

Kara karanta wannan

Sokoto: Sakataren gwamnati ya shiga jarabawa, 'yarsa da jikoki 3 sun rasu lokaci daya

Ciyamomi 2 da kansiloli sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa shugabannin kananan hukumomi biyu da kansiloli 13 sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Shugabannin APC reshen jihar Edo sun tarbe su hannu bibbiyu, sun sahida masu cewa ba za a nuna masu banbanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262