Jam'iyyar PDP Ta Yi Magana kan Gwamnan da Ake Tsoron Zai Sauya Sheka zuwa APC
- Gwamnan jihar Delta, Sherrif Oborevwori na ɗaya daga cikin gwamnonin PDP da aka fara yaɗa jita-jitar za su koma jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Delta ta musanta jita-jitar, ta ce wasu ƴan zaman kashe wando ne suka kirkiro domin ɗauke hankalin jama'a
- PDP a bukaci al'umma su yi fatali da rahoton, inda ta tabbatar da cewa mai girma gwamna na nan daram a jam'iyya mai alamar lema
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Jam'iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa gwamnan jihar Delta, Sherrif Oborevwori ya kammala shirin komawa APC.
Jam'iyyar PDP reshen Delta ta bayyana jita-jitar da ake yadawa a kafofin sada zumunta a matsayin mugunta kuma wacce ba ta da tushe ballantana makama.
A cewarsa, wasu ƴan zaman kashe wando ne da ba su san komai a siyasa ba, aka ɗauke su haya suke yaɗa wannan karerayin, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta musanta batun sauya shekar gwamna
PDP ta bayyana waɗanda suka kirkiro jita-jitar da masu ɗaukar nauyinsu a matsayin masu yunƙurin tayar da rikici a tsakanin al'umma.
Shugaban PDP na jihar Delta, Cif Solomon Arenyeka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin, 6 ga watan Janairu, 2024.
Ya kuma yi kira ga ɗaukacin mazaunan Delta da sauran ƴan Najeriya su yi fatali da wannan jita-jita da ya kira ta mugunta.
Gwamnan Delta na shirin komawa APC?
Sanarwar ta ce:
“Jam’iyyar PDP reshen Delta ta samu labarin wata jita-jita da ake yaɗawa musamman a soshiyal midiya cewa gwamnanmu kuma jagoranmu, Mai Girma Rt. Hon. Sheriff Oborevwori, ya gama shirin komawa APC.
“PDP ta san wannan jita-jita ba ta da tushe kuma aiki ne na wasu ƴan zaman kashe wando da masu ɗaukar nauyinsu da ba su san komai ba a siyasa, waɗanda suka saba tayar da rikici.
"Muna sanar da cewa masu yaɗa wannan karerayin da suke kiran kansu ƴan PDP masu kishin jam'iyya ba su da wata alaƙa da jam'iyyarmu mai albarka.
Jam'iyyar PDP ta kuma yi Allah-wadai da wannan kage da ake yaɗawa kuma ake jingina ta da Gwamna Oborevwori, tana mai cewa yana nan daram a jam'iyyar.
PDP ta bayyana wanda ya kirkiro jita-jitar
Ta ce wanda ya ɗauki nauyin yaɗa jita-jitar gwamna zai sauya sheƙa zuwa APC, wani shahararren maƙaryaci ne da tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba saboda ƙarya.
"Muna kira ga al'umma su yi watsi da wannan jita-jita domin an kirƙire ta ne domin ɗauke hankalin gwamna daga ayyukan alherin da yake yi karkashin ajendar M.O.R.E."
"Babu abin da zai karkatar da tunanin mai girma gwamna daga ayyukan da ya fara na samar da ababen more rayuwa da sauƙaƙawa talakawa a faɗin Delta," in ji PDP.
PDP ta hango nasara a zaɓen 2027
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa ya bayyana cewa yana hangen nasarar jam'iyyar a babban zaɓe mai zuwa.
Kwamitin NWC ya ce duba da halin ƙuncin da ake ciki, ƴan Najeriya sun gaji da mulkin jam'iyyar APC kuma za su iya juya mata baya a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng