Gwamna Bala Ya Fatattaki Kwamishinoni 5 a Gwamnatinsa, Ya ba da Sunayen Sababbi 8

Gwamna Bala Ya Fatattaki Kwamishinoni 5 a Gwamnatinsa, Ya ba da Sunayen Sababbi 8

  • Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa domin inganta shugabanci da tabbatar da nagartaccen aiki ga al'umma
  • Sanarwa ta bayyana cewa an tsige kwamishinonin ne domin kawo sababbin dabaru da kuzari don magance kalubalen da ke gaban gwamnati tare da kyautata ayyuka
  • An tura sunayen mutane takwas don tantancewa a matsayin sababbin kwamishinoni, yayin da gwamnan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta rayuwar al'umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da sauye-sauye a gwamnatinsa tare da tsige wasu kwamishinoni guda biyar.

Gwamnan ya ce ya dauki wannan mataki ne domin inganta shugabanci a gwamnatinsa da tabbatar da nagartaccen aiki.

Gwamna ya sallami kwamishinoninsa 5 tare da maye gurbinsu nan take
Gwamna Bala Mohammed ya kori kwamishinoni 5 inda ya ba da sunayen sababbi guda 8. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Facebook

Gwamna Bala ya sallami kwamishinoni 5

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnatinsa, ya shawarci sabon kwamishina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukhtar Gidado ya bayyana cewa gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin kawo cigaba da inganta harkokin gwamnati.

A cikin sanarwar, Gidado ya ce mai gidansa ya fatattaki kwamishinoni biyar saboda kawo sababbin dabaru a cikin gwamnati.

“A cikin wannan tsari, an tsige kwamishinoni biyar, wanda ke nuna kudirin gwamnati na kawo sababbin tunani da kuzari a shugabanci.”
“Wadanda aka tsige sun hada da Kwamishinar Ilimi, Jamila Dahiru da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Abdulhameed Bununu da Kwamishinan Yada Labarai, Usman Danturaki.”
“Haka nan kuma akwai Kwamishinan Aikin Gona, Madugu Yalams, da Kwamishinan Addini da Gyaran Al’umma, Yakubu Ibrahim."

- Mukhtar Gidado

Gwamnan ya godewa tsofaffin kwamishinonin

Gwamna Bala ya gode wa kwamishinonin da aka tsige bisa gudunmawar da suka bayar wajen cigaban jihar Bauchi da manufofin gwamnatinsa.

Sanata Bala ya kuma bayyana irin gudunmawar da korarrun kwamishinonin suka bayar a gwamnatinsa.

“Ayyukansu sun taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da muhimman manufofi da tsare-tsaren wannan gwamnati."

Kara karanta wannan

Kwamitin kudirin haraji ya gana da malamai 120 domin neman goyon baya

- Cewar sanarwar

Sanata Bala ya tura sunayen sababbin kwamishinoni

Gwamna Bala ya kuma aika sunayen wasu mutane takwas domin tantancewa da amincewa da su a matsayin kwamishinoni a majalisar dokokin jihar Bauchi.

Wadanda aka mika sunayensu sun hada da Babayo Tilde da Abdullahi Mohammed da Bala Lukshi da Usman Shehu da Iliyasu Gital da Titus Ketkukah.

Sauran waɗanda aka tura sunayensu sun hada da Adamu Babayo Gabarin da Mohammed Lawan Rimin Zayam.

Sanarwar ta kara da cewa gwamna Bala ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kyautata rayuwar al’umma tare da cimma manufofin ci gaban jihar Bauchi.

Radda ya yi sauye-sauyen mukamai a gwamnatinsa

Kun ji cewa Gwamnan Dikko Umaru Radda na jihar Katsina, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa don inganta manufofin gwamnatinsa da shugabanci nagari.

Daga cikin sauye-sauyen akwai sabon kwamishina da aka nada, Alhaji Malik Anas a matsayin wanda zai jagoranci ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Kwamitin gwamnatin Tinubu ya karyata zargin dattawan Arewa

Kafin nadin na shi Alhaji Malik ya kasance tsohon Akanta-janar na jihar Katsina inda gwamnan ya bukaci kwamishinan da aka nada da waɗanda aka sauya wa matsayi su dage wajen kawo ci gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.