PDP Ta Hango Abin da Zai Faru Idan ba Ta Karbi Mulki ba a 2027

PDP Ta Hango Abin da Zai Faru Idan ba Ta Karbi Mulki ba a 2027

  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya nuna ƙwarin gwiwar samun nasara a zaɓukan 2027 da ke tafe
  • Ma'ajin PDP na ƙasa ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun gaji da jam'iyyar APC saboda haka za su juya mata baya a zaɓen 2027
  • Alhaji Ahmed Yayare ya yi hasashen cewa idan PDP ba ta karɓi ragamar mulkin ƙasar nan ba a 2027, hakan zai kawo ƙarshen dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na PDP ya fara hango nasarar da jam'iyyar za ta iya samu a zaɓen 2027.

Kwamitin na NWC ya ba da cikakken tabbaci cewa jam'iyyar za ta ƙara yawan gwamnoninta a jihohi da kuma sake samun mulki a matakin tarayya a shekarar 2027.

PDP ta fara maganar zaben 2027
PDP ta ce za ta samar da gwamnoni masu yawa a 2027 Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Kwamitin na NWC ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin ziyara ga gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a gidansa na Sampou, da ke cikin ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Ana batun tsadar mai, gwamnatin Sokoto ta samar da shirin saukaka zirga zirga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa PDP za ta karɓi mulki a 2027?

Da yake magana a madadin kwamitin NWC, ma'ajin PDP na ƙasa, Alhaji Ahmed Yayare, ya bayyana cewa saboda rashin jin daɗi da ake fuskanta a duk faɗin ƙasa, PDP za ta samar da gwamnonin jihohi masu yawa a shekarar 2027.

"Ƙorafin yunwa da talauci ya yi yawa sosai a ƙasar. APC ba za ta iya fita yawon neman zaɓe ba domin za su sha jifa."
"Jihohi 36 na Najeriya suna neman dawowar PDP. Babu abin da zai hana PDP ta samar da shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 2027."
"Idan PDP ba ta karɓi mulkin ƙasar nan ba, wannan zai iya zama alamar ƙarshen dimokuradiyya a Najeriya."

- Alhaji Ahmed Yayare

Ya kuma yi kira ga gwamnonin jam'iyyar da mambobinta su yi aiki tare cikin haɗin kai domin cimma burinsu, yana mai jaddada bukatar haɗin kai kafin zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

NWC ya jajantawa gwamnan Bayelsa

Kwamitin na NWC ya kuma yi amfani da wannan damar wajen jajantawa Gwamna Diri kan rasuwar Moses Jituboh, da kuma kwamishinan harkokin mata, Misis Elizabeth Bidei, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar..

Sakataren PDP na ƙasa, Ude Okoye, ya tabbatar da jajircewar kwamitin NWC wajen mayar da jam'iyyar zama madadin APC, yana mai cewa PDP ta shirya samar da jagoranci mai kyau.

"Za mu ƙarfafa jam'iyyar kuma mu tabbatar da cewa tana da daraja a wajen dukkanin ƴan Najeriya da gwamnoninta."

- Ude Okoye

Gwamna Diri ya ba da shawara

A cikin martaninsa, Gwamna Diri ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin PDP, inda ya yi kira a samar da jituwa a cikin jam'iyyar domin warware matsaloli ba tare da tunkarar kotu ba.

“A matsayinmu na gwamnonin jihohi, dole ne mu yi aiki tare. Ba zai yiwu saboda la'akari da bambancin siyasa, mu aikata abin da bai dace ba. Idan PDP ta mutu a hannunmu, tarihi ba zai yafe mana ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ɗebo ruwan dafa kansa da ya taɓa ƙimar Atiku, matasa sun masa rubdugu

"PDP ce ta samar mana da dama a cikin siyasa. Ba zai yiwu mu zama mambobin PDP a rana ba, kuma da daddare mu koma wata jam'iyya ba. Idan wani yana ganin kansa ya fi ƙarfin jam'iyyar, ya yi tafiyarsa."

- Gwamna Duoye Diri

PDP ta yi sabon sakatare na ƙasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi sabon sakatare na ƙasa bayan Ude Okeye ya kama aiki a wannan muƙamin.

Sabon sakataren na PDP na ƙasa ya bayyana cewa ya kama aiki ne bisa umarnin kotu wanda ya tsige Samuel Anyanwu daga kan muƙamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng