Rikici Ya Kara Tsanani, An Gano Mai Zuga Gwamna Ya Yi Wa Bola Tinubu 'Rashin Kunya'

Rikici Ya Kara Tsanani, An Gano Mai Zuga Gwamna Ya Yi Wa Bola Tinubu 'Rashin Kunya'

  • Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya mayar da zazzafan martani ga tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili
  • Wike ya yi iƙirarin cewa Odili ne ya zuga Gwamna Fubara ya ruguza sulhun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya masu a bara
  • Nyesom Wike ya ce jihar Ribas ba ta tama samun gwamna mai nagarta kamarsa ba kuma ba shi da niyyar maida jihar kadararsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya zargi tsohon gwamnan Ribas, Oeter Odili da zuga Gwamna Siminalayi Fubara ya yi wa Bola Tinubu rashin kunya.

Wike ya ce Odili ne ya shiga ya fita ya ruguza sulhun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi tsakanin tsaginsa da Gwamna Fubara.

Wike da Gwamna Fubara.
Wike ya zargi tsohon gwamnan Ribas, Peter Odili ɗa zuga Gwamna Fubara ya ƙi bin umarnin Tinubu Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Punchi ta ce ministan ya bayyana haka ne a wurin liyafar da aka shirya ta karɓar baƙuncin wasu daga cikin masu ruwa da tsakin Ribas ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin Ministan Abuja da Gwamna Fubara

An dade ana gwabza fadan siyasa tsakanin Fubara da Wike biyo bayan rashin jituwar da ke tsakanin abokanan juna biyu, wadanda yanzu suka koma gaba.

Ɓangarorin biyu sun sa hannu a wata yarjejeniyar zama lafiya a taron sulhun da Bola Tinubu ya jagoranta wanda Peter Odili ya halarta a fadar shugaban ƙasa.

Sai dai yarjejeniyar zaman lafiya ta wargaje, inda Fubara ya yi zargin cewa yaudararsa aka yi ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da tsagin Wike.

Wike na neman maida Ribas kadararsa

Peter Odili, wanda ya yi shekara takwas a kujerar gwamnan jihar Ribas, ya zargi Wike da nuna son kai, rahoton Leadership.

Da yake jawabi a wani taron a Fatakwal ranar 28 ga watan Disamba, Odili ya yabawa Gwamna Fubara da ya hana Wike mayar d Ribas tamkar kadararsa.

Ministan Abuja ya mayar da martani

Amma minsitan Abuja, Wike ya mayar da zazzafan martani ga Odili ranar Juma'a, yana mai jaddada cewa jihar Ribas ba ta faɓa yin gwamna kamarsa ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon abin da mutane suka yi wa Bola Tinubu bayan gama sallah a masallacin Juma'a

“Ina kokarin mayar da Ribas cibiyar kuwon lafiya ta Kudu-maso-Kuducin Najeriya. Ta yaya a yanzu kuma zan dawo na yi kokarin kwace jihar ta zama kadarata?
"Ribas ba ta taɓa samun nagartaccen gwamna kamar ni ba, taya zan maida jihar kadarata? Mutane ba za su iya amsa tambaya mai sauki ba," in ji Wike.

Fubara ya ce ba mai jure wulakancin da ya sha

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Fubara ya ce babu wani gwamna da zai iya jure wulaƙanci da zagin da mutanen Wike suka yi masa.

Siminalayi Fubara ya ce dukkan ƴan majalisar dokokin Ribas da suka sauya sheka zuwa APC sun ra kujerunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262