Ciyamomi 2 da Ƴan Majalisa Sama da 10 Sun Fice daga PDP zuwa Jam'iyyar APC
- Shugabannin kananan hukumomi biyu da kansiloli 13 sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC da ta karbi mulki a jihar Edo
- Masu sauya sheƙar sun ce matakan da Monday Okpebholo ya dauka tun a ranar da ya karɓi mulki ne suka ja hankalinsu zuwa APC
- Shugaban APC na Edo, Emmanuel Ogbomo da sakatare, Injiniya Lawrence Okah ne suka tarbi masu sauya shekar a taruka daban-daban
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Yunƙurin jam’iyyar APC na karɓe ragamar mulki a kananan hukumomi 18 na jihar Edo ya ɗauki sabon salo a ranar Juma’a 3 ga watan Janairu, 2025.
Shugaban ƙaramar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma, Hon. Edosa Enowoghomenma tare da kansiloli takwas sun fice daga PDP zuwa APC.
Kansilolin waɗanda su ne ƴan majalisar ƙaramar hukuma sun sauya sheƙa zuwa APC tare da shugabansu, Hon. Nosakhare Edobor, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC na Ovia, Emmanuel Ogbomo, shi ne ya karɓi ciyaman din da kansiloli takwas a karamar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma.
Ciyaman da ƴan majalisarsa sun shiga APC
Haka nan kuma shugaban ƙaramar hukumar Owan ta Yamma, Hon. Dickson Ahonsi, tare da kansiloli biyar sun bi sahu, sun tattara sun koma APC daga PDP.
Duk wannan sauya sheƙa dai na zuwa ne a lokacin da rikici tsakanin ciyamomin kananan hukumomin Edo da Gwamna Monday Okpebholo ke ƙara ta'azzara.
Da yake jawabi, Hon. Ahonsi ya ce dalilin da ya sa suka yanke shawarar shiga APC shi ne matakan da Gwamna Okpebholo ya ɗauka don ci gaban Edo.
Menene dalilin da ya sa suka koma jami'yyar APC?
Dickson Ahonsi ya ce:
“Da farko, matakan da ya ɗauka a ranar rantsuwar kama aiki sun burge mu sosai, domin ya naɗa muhimman mukamai ba kamar gwamnatin baya ba.
"Kuma nan ba da daɗewa ba, zai fitar da jerin sunayen kwamishinoni, wannan ci gaba ne mai kyau, Ayyukan da ya fara sun nuna fili cewa Edo tana hannun kwararre, shi ya sa muka shiga APC.”
Kofar jam'iyyar APC a buɗe take ga kowa
Da yake karbar masu sauya shekar, sakataren APC na jihar Edo, Injiniya Lawrence Okah, ya bayyana cewa kofofin jam'iyyar a buɗe take ga duk mai son shiga.
Okah ya ce:
“Mun dade muna jiran ku zo mu haɗu a inuwa ɗaya. APC yanzu tana da kansiloli biyar kuma da yawa za su biyo baya. Ku yi amfani da tsintsiya wajen wayar wa mutane kai su shiga jam’iyyar.”
Ɗan majalisar Edo ya koma jam'iyyar APC
Kun ji cewa Hon Ojezele Osezua Sunday mai wakiltar mazaɓar Esan ta Kudu maso Gabas a Majalisar dokokin Edo ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa bar jam'iyyar PDP ne saboda rikicin cikin gida da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a babbar jam'iyyar adawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng