Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa da Ya Taɓa Ƙimar Atiku, Matasa Sun Masa Rubdugu
- Kalaman da Kwankwaso ya yi cewa Atiku Abubakar maƙaryaci ne sun harzuƙa matasa masu goyon bayan Wazirin Adamawa
- Ƙungiyar NYFA ta gargaɗi jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya daina taɓa mutuncin Atiku
- Ta ce bai kamata a rika jin kalamai marasa daɗi daga shugabannin adawa a wannan lokacin da ake kokarin haɗakai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƙungiyar matasa magoya bayan Atiku (NYFA) ta gargaɗi jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso da ya daina cin mutuncin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Daraktan sadarwa na NYFA, Mista Dare Dada, ne ya yi wannan gargaɗi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a jihar Lagos.
Dada dai ya yi martani ne ga wata hira da Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023 ya yi da manema labarai kwanan nan, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya taɓa ƙimar Atiku Abubakar
A cikin hirar, Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa ƴan tsagin Atiku sun yaɗa ƙarya cewa sun cimma wata yarjejeniya da shi da Peter Obi, cewa za su rika karɓa-karɓar mulkin Najeriya daga 2027.
Haka nan kuma a hirar an ji Kwankwaso na cewa ya kamata Atiku Abubakar ya san girma ya kama shi, ya daina ƙarya a shekara 80.
Da yake mayar da martani ga Kwankwaso, kakakin kungiyar matasan Atiku, Dada ya musanta wannan iƙirarin, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
Matasa sun yi wa Kwankwaso ca kan Atiku
Mista Dada ya ƙara cewa:
“Abin takaici ne cewa wani kamar Kwankwaso zai yi ƙoƙarin cin mutuncin Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa, don kawai ya ƙara matsayi a siyasa.
“Yin ƙarya don neman suna a siyasar Najeriya ba kawai abin dariya ba ne, abin kunya ne."
Kakakin NYFA ya ce bai kamata ana zagin jagororin adawa ba a wannan lokaci da ake kokarin haɗa kai wuri guda domin samar da mafita ga ƴan Najeriya a 2027.
Abin da ya kamata Kwankwaso ya yi
Dare Dada ya ce ya kamata shugabannin adawa su guji kalaman raba kawuna, waɗanda za su iya kawo cikas ga haɗin kai da ci gaban da ake buƙata a ƙasar nan.
Shugaban matasan ya yi kira ga Kwankwaso da ya karkatar da hankalinsa ga matsalolin da ke damun Arewacin Najeriya.
PDP na shirin jawo Kwankwaso cikinta
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce za ta tuntuɓi Rabiu Kwankwaso kuma tana sa ran zai amince ya dawo cikinta gabanin zaɓen 2025.
Muƙaddashin shugaban APC na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi kwanan nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng