'Ba Mai Jure Wulakancin da Ku ka Yi Mani': Gwamna ga Tsohon Mai Gidansa, Ya Bugi Kirji

'Ba Mai Jure Wulakancin da Ku ka Yi Mani': Gwamna ga Tsohon Mai Gidansa, Ya Bugi Kirji

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa 'yan majalisar PDP da suka sauya sheka zuwa APC sun rasa kujerunsu dindindin
  • Fubara ya ce babu wata majalisa da ta wanzu a jihar sai wanda Victor Oko-Jumbo ke jagoranta tare da sauran ‘yan majalisarsa uku
  • Ya jaddada cewa ya sha wulakanci daga mutanen Nyesom Wike amma yanzu burinsa shi ne kare muradun jihar Rivers da tabbatar da gaskiya a mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan rigimarsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike a jihar.

Fubara ya kare matakinsa na gabatar da kasafin kudin 2025 ga ‘yan majalisar da suka rage guda uku kacal.

Fubara ya ja kunnen Wike kan cin mutuncin da ake masa
Gwamna Siminalayi Fubara ya sha alwashin daukar mataki kan cin mutuncinsa game da Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Fubara ya fadi makomar yan majalisun Rivers

Punch ta ce Fubara ya bayyana cewa sauran mambobin 27 na majalisar jihar, wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC, sun rasa kujerunsu har abada.

Kara karanta wannan

An ware biliyoyi domin yin hidima ga Akpabio, Barau da sauran shugaban majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, babu wata dama da zata sa wadannan ‘yan majalisar da suka bi tsohon gwamna Nyesom Wike su koma kujerunsu a majalisar jihar.

Fubara, wanda ke cikin rikici da Wike, ya ce ya gaji da wulakancin da ke fitowa daga sansanin Wike kuma ba zai sake yarda da hakan ba.

Da yake jawabi bayan rattaba hannu kan kasafin kudin Naira tiriliyan daya da biliyan dari daya na 2025, Fubara ya ce babu wata majalisa ta daban a jihar.

Ya jaddada cewa majalisar da Victor Oko-Jumbo ke shugabanta ita ce kadai halastacciya, cewar Premium Times.

“Ina son bayyana wannan don mutane su fahimta, akwai majalisa daya ne kawai kuma ta Victor Oko-Jumbo ce."
"Wata tafiyar munafurci da suka fara watanni tara da suka wuce yanzu ta ruguje, ba za mu janye ba."

- Siminalayi Fubara

Fubara ya yi alkawari ga mutanen Rivers

Kara karanta wannan

Wike ya tsokano tsuliyar dodo da ya tabo tsohon gwamna, ya sha rubdugu

Fubara ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da kare mutuncin jihar Rivers da tabbatar da gaskiyar shugabanci.

Ya kuma yaba wa ‘yan majalisar jihar da sauran jami’an gwamnati bisa kokarinsu wajen tabbatar da ci gaban jihar.

An ja kunnen Wike kan taba Odili

Kun ji cewa Dattawan jihar Rivers sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya nemi gafarar kalaman batanci da suka ce ya yi wa tsohon gwamna, Dr. Peter Odili.

An ruwaito cewa dattawan sun bayyana cewa kalaman Wike sun sabawa dabi’un girmama dattawa da mutuntawa da jihar Rivers ta yi kaurin suna da su.

Sun yabawa Odili a matsayin shugaba mai biyayya wanda ya hakura da takarar shugaban kasa a 2007 domin daidaito tsakanin yankin Arewa da Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.