Tinubu: Kalaman Peter Obi Sun Yi wa APC Zafi, Ta Zarge Shi da Son Tunzura Jama'a

Tinubu: Kalaman Peter Obi Sun Yi wa APC Zafi, Ta Zarge Shi da Son Tunzura Jama'a

  • Kalaman tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi sun yamutsa hazo bayan ya ba gwamnatin Bola Tinubu shawara
  • Obi ya ce akwai bukatar Tinubu ya daina zuwa kasashen waje neman lafiya, sannan ya rika bin titunan kasarsa lokaci zuwa lokaci
  • APC ta yi masa zazzafan martani, inda ta zargi Obi da son jawo wa gwamnatin tarayya bakin jini duk da kokarin da ta ke yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam’iyya mai mulki ta APC ta soki kalaman tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi a kan jerin shawarwari da sukar gwamnatin Bola Tinubu.

A ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis, Mista Peter Obi, ya yi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya rika neman lafiya a asibitocin Najeriya .

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Peter
APC ta yi wa Obi martani Hoto: Mr. Peter Obi/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a martaninta, APC ta zargi tsohon dan takarar da son tayar da tarzoma da jawo wa gwamnati bakin jinni duk da kokarin da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta karyata ikirarin Peter Obi

Jam’iyyar APC ta karyata ikirarin da Peter Obi ya yi na cewa gwamnati ta gaza magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da suka kara tabarbarewa cikin watanni 18 na mulkinsa.

Jam’iyyar, ta cikin sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Felix Morka ya fitar ya gargadi tsohon dan takarar da ya guji fadi kalaman da za su harzuka jama’a da mulkin Tinubu.

APC ta ja kunnen Peter Obi

APC ta ce babu kamshin gaskiya a kalaman Obi na cewa sakon sabuwar shekara da shugaban kasa, Tinubu ya fitar na cike da yaudara, tare da shawartarsa a kan salon jagorancin kasa.

Jam’iyyar ta gargadi Obi a kan irin wadannan kalamai, ta zarge shi da zama daya daga cikin masu fadin rashin alherin gwamnati duk da alamu sun tabbatar da ana samun ci gaba.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

Obi ya yi bayanin shirin tadiye APC

A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya yi karin bayani a kan shirin jam'iyyun adawa na hade kai domin kawar da APC daga mulkin Najeriya.

Mista Obi ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga kulla wata yarjejeniya a kan hakan ba, amma ya yi kira ga sauran jam'iyyun adawa su taho a hade wuri guda domin fatattakar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.