Kwankwaso da Wasu Ƙusoshin Siyasa 3 da Suka Fi Yin Tasiri a 2024 a Najeriya

Kwankwaso da Wasu Ƙusoshin Siyasa 3 da Suka Fi Yin Tasiri a 2024 a Najeriya

  • Fagen siyasar Najeriya cike yake da manyan mutane masu karfin faɗa a ji da tasiri a jam'iyyun siyasa daban-daban
  • Sai dai duk da haka, wasu mutum hudu daga ciki sun yi fice a shekarar 2024, inda suka banbanta kansu da sauran ƴan siyasa
  • Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi na daga cikin manyan 'yan siyasar Najeriya suka yi tashe a 2024 kamar yadda muka yi nazari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, cnishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu daga cikin manyan ƴan siyasa a Najeriya sun banbanta kansu da saura ta hanyar nuna karfin tasiri da faɗa aji a shekarar 2024.

Bisa al'adar siyasar kasar nan, manya daga ciki kan kokarin nuna tasirin da suke da shi a jam'iyyarsu da sauran jam'iyyu, kai har ma da wajen jihar da suka fito.

Kara karanta wannan

"Ka fito ka faɗawa mutane gaskiya," Peter Obi ya kwancewa Tinubu zani a kasuwa

Shugaba Tinubu, Kwankwaso da Peter Obi.
Shugaba Tinubu na cikin manyan ƴan siyasa masu ƙarfin tasiri a 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

A yayin da ake bankwana da 2024, Legit.ng ta zaƙulo maku wasu ‘yan siyasa, jagorori, kuma waɗanda suka girgiza harkar siyasar Najeriya a 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu

Ɗan ƙasa lamba ɗaya, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu shi ne ɗan siyasar da ya fi yin fice da tasiri a siyasar Najeriya a shekarar 2024.

Bayan ya lashe zaben shugaban kasa a 2023, tasirin Shugaba Tinubu ya ci gaba da karuwa, har ma da jam’iyyarsa ta APC mai mulki da kuma yankin Kudu maso Yamma.

Siyasar tsohon gwamnan jihar Legas ta samu ci gaba a 2024 duba da yadda ƴan majalisu da manyan jiga-jigai suka shiga jam'iyyarsa ta APC, rahoton Daily Trust.

2. Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi

Kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin matasa da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ba ta ci gaba da haɓaka ba duk da ya sha kaye hannun Tinubu a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kan siraɗi": Peter Obi ya yi magana kan haɗa kai da Kwankwaso da Atiku

Har yanzun, galibin matasa musamman a Kudu maso Gabas suna kallon Peter Obi a matsayin wani fata na sauya akalar siyasar Najeriya.

Tasirin tsohon gwamnan jihar Anambra ya yaɗu zuwa kabilu da addinai, inda ya ci gaba da zaburar da matasa a salon siyasarsa na musamman.

3. Ministan Abuja, Nyesom Wike

Ministan harkokin babban birnin tarayya, Nyesom Wike, na daya daga cikin masu haskawa a gwamnatin shugaba Tinubu.

Duk da rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa Gwamna Simi Fubara, har yanzu Wike ne ke rike da tsarin siyasa a jam'iyyar PDP ta jihar Ribas.

Tasirinsa ya sa aka nada shi minista a gwamnatin jam'iyyar APC duk da kasancewarsa dan babbar jam'iyyar adawa watau PDP.

Ayyukan Wike ta fuskar samar da ababen more rayuwa a babban birnin kasar nan ya sa mazauna Abuja da maziyarta kaunarsa duk da dai akwai masu sukarsa.

4. Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan

Tinubu ya dawo da tsarin makarantun Najeriya da aka soke lokacin yana gwamna

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso shi ne uba a siyasar jihar Kano.

Kamar guguwa haka Kwankwasiyya ta ƙwace mulkin jihar Kano daga hannun APC a babban zaɓen 2023 duk saboda karfin siyasa da faɗa aji na Kwankwaso.

A ƴan kwanakin nan, Kwankwaso ya ce zai ruguza tasirin APC a jihar Kano ta yadda ba za ta samu ƙuri'u da yawa ba a zaɓen 2027.

Yayin da ƴan majalisun tarayya na LP ke sauya sheka zuwa APC, har yanzu ƴan NNPP na nan daram a jam'iyyarsu, ana ganin hakan ba zai rasa nasaba da tasirin Kwankwaso ba.

5. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar na ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka yi tashe a shekarar 2024 a Najeriya.

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP a zaɓen 2023 yana da mabiya a lungu da saƙon ƙasar nan kuma harzu yana cikin waɗanɗa ake ganin za su iya kayar da Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Bayan rashin nasara a 2023, babu wani ɗan siyasa da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu kamar Atiku musamman a abubuwan da yake ganin an yi kuskure.

Ba a jima ba da Atiku ya fito a shafinsa na X, ya soki tulin kuɗin da Bola Tinubu ya ce zai karɓo bashi domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025.

Kwankwaso ya gano manufar masu zuga Abba

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan masu kiraye-kirayen 'Abba tsaya da ƙafarka;.

Jagoran NNPP na ƙasa ya ce duk masu ba gwamna Abba Yusuf shawarar da ya bar tafiya Kwankwasiyya suna da wata manufa kuma ba alheri ba ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262