Gwamna Ya Yi Cuku Cuku, Ya Runtumo Bashin Maƙudan Kudi a Asirce? Bayanai Sun Fito

Gwamna Ya Yi Cuku Cuku, Ya Runtumo Bashin Maƙudan Kudi a Asirce? Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya musanta zargin da ake cewa ya karɓo bashin makudan kuɗi a asirce
  • Gwamnan na jam'iyyar PDP ya ce zargin wanda APC ta yi ba shi da tushe balle makama, ya ce duk tatsuniya ce da aka kirkiro
  • Mai magana da yawun gwamnan, Olawole Rasheed ya ce mai girma gwamna bai sa hannu a ciyo bashin kudi ba tun da ya kafa gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya karyata zargin da jam’iyyar APC ta yi na cewa gwamnatin jihar na karbar rance maƙudan kudi a asirce.

APC a jihar Osun dai ta kalubalanci Adeleke ya fito ya bayyana haƙiƙanin alkaluman asusun gwamnati idan har yana kishin talakawan da ke cikin matsi.

Gwamna Adeleke.
Gwamna Adeleke ya musanta zargin karbo bashi a sirrance a jihar Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

APC ta zargi gwamna da karɓo bashi a asirce

Kara karanta wannan

"Muna sa rai Kwankwaso zai dawo cikinmu," PDP na son kwace mulki daga hannun Tinubu

Jam'iyyar ta kalubalanci gwamnan a yayin taron manema labarai na karshen shekara da ta gudanar a Osogbo ranar Litinin, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yada labarai na APC, Kola Olabisi, ya zargi gwamnatin Adeleke da sanya hannu a asirce tare da karbar rancen kudin da suka kai dala miliyan 51, kwatankwacin Naira biliyan 81.6.

Olabisi ya jaddada cewa gwamnatin Adeleke na daf da jefa makomar jihar cikin wani mawuyacin hali, ya yi kira ga al’ummar Osun da su tashi tsaye.

Gwamna Adeleke ya musanta ikirarin APC

Sai dai a martanin da ya mayar, mai magana da yawun gwamna Adeleke, Olawale Rasheed, ya yi watsi da ikirarin na jam'iyyar APC, ya kira shi da tatsuniya.

Ya jaddada cewa Gwamna Adeleke bai amince da karbo rancen ko kwandala ba tun da ya hau kan karagar mulki.

"A matsayina na ɗan majalisar zartarwa tun daga farkon kafa gwamnati, ina tabbatar da cewa ba a nemi runtumo bashi da nufin yin kowane aiki ba.

Kara karanta wannan

Akpabio: Gaskiyar abin da ya sa shugaban majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC

"Wannan labari ne na karya, wanda APC ta saba yi, mutanen Osun suna da hankali kuma suna da ilimi, sun san lokacin da gwamnatinsu ke karbar bashi," in ji Rasheed.

Olawale Rasheed ya kuma musanta zargin cewa jihar Osun ta runtumo bashin kudi daga kasashen waje a karkashin shirin NG-CARES, Daily Post ta ruwaito.

Gwamna ya nuna kauna ga talakawansa

A wani labarin kun ji cewa Gwamna Adeemola Adeleke ya ce duk da yana kaunar rawa a rayuwarsa, amma sauke nauyin talakawa ya fi faranta mada rai.

Gwamnan ya tabbatarwa al'ummar jihar Osun cewa ayyukan tituna, gina makarantu da sauran ababen more rayuwa da ya fara sun kankama a kowane yanki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262