El Rufa'i, Omokri da Shehu Sani Sun Fara Harbin Juna da Maganganu kan Tinubu
- Rikicin siyasa ya kaure tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon hadimin Goodluck Jonathan, Reno Omokri
- Nasir El-Rufai ya maida martani kan zargin da Reno Omokri ya masa na cewa ya fusata ne saboda rashin samun shiga gwamnatin Tinubu
- Martanin tsohon gwamnan ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan jam’iyyar APC da wasu ‘yan siyasa a Kudu da Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kwatanta tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan a matsayin mai neman kwangilar siyasa.
Martanin ya biyo bayan zargin da Omokri ya yi masa na nuna damuwa kan rashin samun mukamin minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Legit ta gano cewa Reno Omokri ya wallafa a shafinsa na X cewa El-Rufai ya soki gwamnatin Tinubu ne kan rashin samun mukami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korafe-korafen Omokri da martanin El-Rufai
Reno Omokri ya yi magana kan sukan wani shirin gwamnatin tarayya na gina layin dogo a Lagos da El-Rufa'i ya yi, yana mai cewa bai yi irin korafin ba lokacin Buhari.
El-Rufa'i ya yi martani a Facebook inda ya yi nuni da cewa Omokri ya taɓa yin zargi marar tushe kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi.
Punch ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya yi ishara da zargin cewa Omokri ya taba amfani da sunan bogi, Wendell Simlin, domin jingina Sanusi Lamido Sanusi da Boko Haram.
El-Rufa'i: Ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa
Martanin El-Rufai ya ja hankalin ‘yan siyasa ciki har da tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, wanda ya zargi Nasir El-Rufai da rashin gaskiya.
Shehu Sani ya wallafa a X cewa El-Rufai bai yi korafi ba lokacin da gwamnatin Buhari ta ke nuna bambanci wajen raba mukamai.
Ya kara da cewa jihar Kaduna ta zama kamar jihar wariya karkashin El-Rufai na tsawon shekaru takwas.
Tinubu ya yi martani ga gwamnan Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya janye kalaman da ya yi kan Bola Tinubu dangane da haraji.
Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya ce kalaman da gwamnan ya yi ba su da ce da mutum mai matsayi irin na shi ba a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng