Akpabio: Shugaban Majalisa Ya Cika Baki, Ya Fadi Jihohin da APC Za Ta Kwace a 2027
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya taɓo batun shirin jam'iyyar APV kan yankin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027
- Godswill Akpabio ya bayyana cewa ta shirya lashe sauran jihohi huɗu da ba su ƙarƙashin ikonta a zaɓen 2027 mai zuwa
- Akpabio ya bayyana cewa tun da farko ya koma APC ne domin ganin ya jawo mutanen yankin zuwa cikinta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce jam’iyyar APC mai mulki a shirye take ta lashe dukkanin jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027 mai zuwa.
Godswill Akpabio ya kuma bayyana zaɓen Monday Okpebholo a gwamnan jihar Edo matsayin wanda Allah ya tsara domin kawo ɗauki ga al’ummar jihar.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamna Monday Okpebolo a gidansa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin jihohi shida na shiyyar Kudu maso Kudu, APC tana mulki ne kawai a Edo da Cross Rivers.
Meyasa Akpabio ya koma jam'iyyar APC?
Akpabio ya bayyana cewa dalilin sauya sheƙar sa zuwa jam’iyyar APC, shi ne domin ya dawo da ɗaukacin yankin Kudu maso Kudu zuwa jam’iyya mai mulki.
"A gwamnatin APC, da yawa daga cikinmu sun yanke shawarar cewa akwai buƙatar mu sauya sheƙa, domin samun damar wakiltar jama’armu a matakin ƙasa da kuma faɗin albarkacin bakinmu kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan."
"Domin haka, lokacin da na koma zuwa jam’iyyar APC, na yi ne domin kai mutanenmu a yankin Kudu maso Kudu zuwa gwamnatin da ke sama."
"Duba da lissafe-lissafen da ake yi yanzu, bisa ga dukkan alamu, jam'iyyar APC mai mulki a shirye take ta kawo ƙarin jihohi da ke ƙarƙashin ikonta."
- Godswill Akpabio
Ƴan adawa sun koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dubunnan ƴan adawa daga jam'iyyu daban-dabaan sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar Abia.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya tarbi masu sauya sheƙar zuwa jam'iyyar APC waɗanda adadinsu ya kai mutum 3,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng