2027: Jigo a PDP Ya ba Jam'iyyar Mafita kan Zaben Shugaban Kasa
- Wani ƙusa a jam'iyyar PDP a jihar Legas ya taɓo batun takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
- Adetokunbo Pearse wanda mamba ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a 2023, ya buƙaci ka da PDP ta ba ɗan Arewa takara a 2027
- Jigon na PDP ya nuna cewa abin da ya kamata jam'iyyar ta yi shi ne ta tsayar da ɗan Kudu a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Legas kuma tsohon mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar a 2023, Adetokunbo Pearse, ya ba PDP shawara.
Tsohon mamban na kwamitin yaƙin neman zaɓen na Atiku ya buƙaci jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa ɗan Kudu ya fito a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.
Adetokunbo Pearse ya ba da wannan shawarar ne a wata hira da manema labarai a Legas ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon PDP ya ba jam'iyyar shawara
Ya bayyana cewa mai yiwuwa ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa ba zai zama alheri ga jam’iyyar ba a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
"A halin da ake ciki a yanzu, abin da ake cewa shi ne cewa PDP ta tsayar da ɗan Kudu a matsayin ɗa takarar shugaban ƙasa a 2027."
"Muna buƙatar wani ɗan Kudu da zai kammala waɗannan shekaru huɗu, domin ya cika shekaru takwas na yankin Kudanci ƙasar nan domin mu ceto Najeriya."
"Wannan shi ne abin da ƴan Najeriya ke cewa a yanzu. Don haka ina da ra’ayin cewa ba dabara ba ne, bai dace mu ce muna goyon bayan ɗan Arewa ya zama shugaban ƙasa ba."
- Adetokunbo Pearse.
Ƙusan na PDP ya kuma ce jam'iyyar ba ta buƙatar hadewa da wata jam’iyyar siyasa domin samun nasara.
PDP ta ƙalubalanci Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ƙalubalanci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bayan ya yi kalaman cewa an samu tsaro a ƙasar nan.
PDP ta buƙaci shugaban ƙasan ya yi tafiya daga birnin Abuja zuwa Legas domin tabbatar da halin da ake ciki, ba wai ya dogara da abin da ake gaya masa ba.
Asali: Legit.ng