APC Ta Samu Tagomashi, Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Tarbi 'Yan Adawa 3,000

APC Ta Samu Tagomashi, Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Tarbi 'Yan Adawa 3,000

  • Jam'iyyar APC ta samu tagomashi a jihar Abia bayan wasu ɗimbin mutane sun sauya sheƙa zuwa cikinta
  • Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, wanda ya tarbe su ya bayyana cewa sun yanke shawara mai kyau da suka shigo APC
  • Benjamin Kalu ya cika bakin cewa nan gaba kaɗan mutane za su yi ta tururuwa suna shigowa jam'iyyar APC a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ya karɓi sababbin mambobin da suka shigo APC daga jam'iyyun adawa.

Benjamin Kalu ya tarbi mambobin sama da 3,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa APC a hukumance a jihar Abia.

'Yan adawa sun koma APC a Abia
Kalu ya tarbi masu sauya sheka zuwa APC a Abia Hoto@ @OfficialBenKalu
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Levinus Nwabughiogu ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauya sheƙar ya auku ne garin Akwete da ke Ndoki a ƙaramar hukumar Ukwa ta Gabas, yayin wani shirin ba da tallafi na Chris Nkwonta, mamba mai wakiltar Ukwa ta Gabas da Ukwa ta Yamma a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘yan siyasa 6 da suka bar adawa, suka koma jam’iyyar APC a shekarar 2024

Kalu ya tarbi masu sauya sheƙa zuwa APC

Da yake jawabi ga ɗimbin jama’an da ke wajen, Kalu ya yi ƙarin haske kan cewa akwai ƙarin masu sauya sheƙa zuwa APC nan gaba, yana mai jaddada tasirin jam’iyyar a yankin.

Kalu ya bayyana guguwar sauya shekar a matsayin wata alama ta nuna godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarin da yake a yankin Kudu maso Gabas, musamman ta hanyar kafa hukumar SEDC.

Kalu ya buƙaci sabbin ƴaƴan jam’iyyar da su jajirce wajen goyon bayan APC, inda ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar za ta ba da fifiko ga walwala da ci gaban su.

"Bisa ɗaukar wannan shawarar ta shigowa APC, za ku ga da kyau. Jam’iyyar za ta ba ku madafa ta yadda kuma za ku tallafi wasu."

- Benjamin Kalu

Kwankwaso ya faɗi shirinsa kan APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana shirinsa a kan jam'iyyar APC a jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana cewa yana son rage tasirin jam'iyyar APC a Kano ta yadda ba za ta yi wani abin a zo a gani ba a zaɓen 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng