Talakawa Sun yi Tururuwa Gidan Tinubu Neman Tallafi, An Caccaki Shugaban Kasa
- Bidiyon jama’a suna tururuwa domin neman tallafi a gidan Bola Tinubu ya jawo caccaka daga jam’iyyun hamayya
- Jam’iyyun adawa sun zargi gwamnatin APC da jefa ‘yan Najeriya cikin talauci da yunwa saboda tsare tsaren da suka kawo
- Shugabannin jam'iyyun adawa sun bukaci a sake dubi kan tsare tsaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyun adawa, musamman LP da PDP sun zargi gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki da kara jefa ‘yan Najeriya cikin talauci.
Caccakar ta zo ne bayan bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga dogayen layukan jama’a suna neman tallafi a layin gidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Bourdillon a Lagos.
Sanata Ali Ndume, wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na X, ya ce lamarin ya nuna irin wahalar da ‘yan ƙasa ke ciki a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Talauci ya jefa mutane sun koma roƙo
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa talaucin da ake ciki ya kai ga kowa yana cikin wahala, ba tare da la’akari da addini, ƙabila, ko jam'iyyar siyasa ba.
“Abin takaici ne ganin dogon layin jama’a suna jiran tallafi a gidan shugaban ƙasa a Bourdillon a daren Kirsimeti. Wannan alama ce ta wahalar tattalin arziki ."
- Ali Ndume
Sakataren yada labaran jam'iyyar LP, Obiora Ifoh ya zargi APC da jefa ƙasar cikin talauci, yana mai cewa talaucin ya sa mutane suna dogaro da tallafi fiye da kima.
Peter Obi: Manufofin APC na talauta jama’a
Dan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa manufofin APC sun jefa Najeriya cikin mawuyacin hali.
Punch ta walafa cewa Obi ya ce manufofin gwamnati ba su taimaka wa rayuwar talakawa ba, kuma hakan alama ce ta gazawa a shugabanci.
Mataimakin Shugaban Matasan PDP, Timothy Osadolor, ya zargi APC da amfani da talauci a matsayin makamin siyasa.
Bukatar sake duba tsarin tattalin arziki
Jam’iyyar YPP ta bayyana damuwa kan yadda tsare tsaren tattalin arziki suka tsananta wahalar da ake ciki.
Sakataren yada labaran YPP, Egbeola Martins, ya yi kira da a sake duba tsare tsaren, musamman cire tallafin mai, yana mai cewa hakan ya kawo wahalar da ake ciki a yau.
Gwamna ya nemi soke kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya kara daukan zafi kan yadda Bola Tinubu ya nace a kan kudirin haraji.
Sanata Bala Mohammed ya ce dole shugaba Tinubu ya saurari jama'a wajen dakatar da kudirin haraji tunda ba a mulkin soja ake ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng