Duk da Rikicin da Ya Addabi PDP, Jam'iyyar Ta Samu Babbar Ƙaruwa gabanin Zaɓen 2027

Duk da Rikicin da Ya Addabi PDP, Jam'iyyar Ta Samu Babbar Ƙaruwa gabanin Zaɓen 2027

  • Jam'iyyar PDP ta samu karuwa a yankin karamar hukumar Itesiwaju ta jihar Oyo ranar Litinin, 23 ga watan Disambar 2024
  • Amofin Beulah Adeoye, masanin harkokin shari'a ya shiga PDP kuma ya tabbatar da shirinsa na neman takarar gwamna a zaɓen 2027
  • Shugabanni da ƴaƴan PDP a karamar hukumar sun yi murna, inda suka tabbatar masa da samun cikakken goyon bayansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Amofin Beulah Adeoye ya shiga jam’iyyar PDP a hukumance ranar Litinin a karamar hukumar Itesiwaju ta jihar Oyo.

Fitaccen masanin doka kuma lauyan ya samu tarba mai kyau daga shugabanni da ƴaƴan PDP na ƙaramar hukumar Itesiwaju.

Amofin Beulah Adeoye.
Jam'iyyar PDP ta samu ƙaruwa, Amofin Beulah ya koma inuwarta a jihar Oyo Hoto: Amofin Beulah Adeoye
Asali: Facebook

Shugaban jam'iyyar PDP na Itesiwaju, Hon. Ganiyu Owolabi, ya bayyana Amofin Adeoye a matsayin dan kasa na gari mai kishi, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Najeriya ta yi babban rashi, tsohon AIG ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta samu babbar ƙaruwa a jihar Oyo

Ya bayyana cewa sai da lauyan ya gana da jagororin PDP na karamar hukuma, na gunduma da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya yanke shigowa jam'iyya mai mulki a Oyo.

Shugaban PDP ya sa albarka a burin Amofin Adeoye na neman takarar gwamna tare da ba shi tabbacin samun cikakken goyon baya daga kowane bangare na karamar hukumar Itesiwaju.

A cewarsa, samun goyon bayan manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP yana da matukar muhimmanci a gare shi idan har yana son cimma burinsa na zama gwamna.

Adeoye yana da burin zama gwamna a PDP

'Dan siyasar ya bukaci ‘yan PDP da mazauna yankin Itesiwaju da jihar Oyo baki daya da su yi wa Amofin Adeoye addu’a domin ganin ya cimma burinsa na siyasa.

Bayan haka ne aka mika masa katin zama ɗan PDP wanda ya kara tabbatar da cewa ya koma inuwar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban APC, Ganduje ya bayyana shirinsu a kan 'yan Najeriya

A nasa jawabin, Adeoye ya ce shirinsa na neman takarar gwamna daga Allah ne kuma ba zai iya tsallake kaddara ba.

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Gwamna Seyi Makinde ya san da zuwa na karamar hukumar Itesiwaju. Ku sani wanna ba aikin mutun ɗaya ba ne, sai mun haɗa kai," in ji shi.

Ɗan majalisa ya bar PDP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan Majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Ojezele Osezua Sunday ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC ranar Litinin.

Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda rikicin da ya addabi PDP, ya ce zai iya ci gaba da zama wurin da babu zaman lafiya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262