2027: APC Ta Fadi Abin da zai sa Tinubu Ya Lashe Kuri'un Arewa ta Tsakiya
- Jam'iyyar APC ta reshen Benue ta bayyana cikakken goyon bayanta ga yiwuwar wa'adin mulki na biyu na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027
- APC ta nuna gamsuwarta da ayyukan sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, tare da jaddada cikakken goyon baya a gare shi
- Manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun bayyana cewa haɗin kai tsakanin Arewa ta Tsakiya da Benue zai tabbatar da nasara ga APC a gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Benue ta nuna cikakken goyon bayan takara ta biyu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Jam’iyyar ta yi jinjina ga sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, tare da nuna gamsuwa da irin gudunmawarsa ga jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa wani tsohon ɗan majalisa na jamhuriya ta biyu, Sanata Jack Gyado ne ya yi bayanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta ce Tinubu zai lashe Arewa ta Tsakiya
Sanata Jack Gyado ya bayyana cewa Sanata George Akume ya cancanci muƙamin SGF tare da jagorancin yankin Arewa ta tsakiya a jam’iyyar APC.
A cewar Gyado, haɗin kai tsakanin yankin Arewa ta tsakiya da sauran shugabanni a jam’iyyar zai tabbatar da cewa Tinubu zai samu nasara a zaɓen 2027.
Haka zalika, Sanata Gyado ya ce haɗin kan jam’iyyar a jihar Benue yana jawo ‘yan siyasa daga PDP da sauran jam’iyyu su shiga APC.
Jam'iyyar APC ta yi magana kan yunkurin tsige Akume
Fitaccen dan siyasa a Benue, Godwin Ityoachimin ya bayyana cewa kira ga sauke Akume daga muƙaminsa ɓata lokaci ne kawai.

Asali: Twitter
Godwin Ityoachiminya ce akwai bukatar nuna goyon baya ga Akume domin ya samu nasara a ayyukan da ya sa a gaba tare da tabbatar da cewa APC ta kara samun nasara.
Bugu da ƙari, Ityoachimin ya yaba wa shugaban ƙasa Tinubu kan jagorancin sa mai kyau, yana mai cewa jihar Benue ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen cigaba da goyon bayan sa.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Austin Agada, tare da sauran shugabanni, sun tabbatar da cewa jam’iyyar APC a Benue za ta ci gaba da zama ɗaya tare da kawo ci gaba ga jihar.
Kiristoci sun yabi kudirin harajin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin addinin Kirista a jihohin Arewa 19 da birnin tarayya Abuja sun goyi kudirin harajin Bola Tinubu.
Legit ta ruwaito cewa shugabannin addinin sun yanke matsayar ne bayan wani taro da suka gudanar a jihar Kaduna a makon da ya wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng