PDP Ta Ƙara Rasa Babban Jigo, Ɗan Majalisa Ya Sauya Sheƙa zuwa Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a majalisar dokokin jihar Edo yau Litinin, 23 ga watan Disamba, 2024
- Hon Ojezele Osezua Sunday mai wakiltar mazaɓar Esan ta Kudu maso Gabas ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulki
- Shugaban APC na jihar Edo, Jaret Tenebe ya yi farin ciki da sauya shekar, ya ce nan da ƴan watanni wasu za su sake shigowa APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jam'iyyar APC ta fara samun ƙaruwa a Majalisar dokokin jihar Edo ƙasa da watanni biyu bayan rantsar da Gwamna Monday Okpebholo.
Ɗaya daga cikin ƴan majalisar Edo, Honarabul Ojezele Osezua Sunday ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, 2024.
Dalilin ɗan Majalosar na komawa jam'iyyar APC
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa ɗan majalisar ya bar PDP ne saboda rigingimun cikin gida da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a babbar jam'iyyar adawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon Ojezele Osezua Sunday, shi ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Esan ta Kudu maso Gabas a Majalisar dokokin Edo.
Ya bayyana farin cikinsa da sake haɗewa da APC, inda ya ce yana jin kamar ya koma gidansa ne na asali.
Shugaban APC ya karɓi ɗan Majalisar a Benin
Shugaban jam'iyyar APC na Edo, Jaret Tenabe ne ya tarɓi ɗan majalisar a hedkwatar jam'iyyar da ke Benin City.
Da yake nuna farin cikinsa na sauya shekar Hon. Monday, Mista Tenebe ya ce wasu manyan ƙusoshi za su dawo APC a watanni masu zuwa.
Wasu ƴan PDP za su dawo jam'iyyar APC
Ya ƙara da cewa babu ruwan APC a rigingimun da suka addabi PDP waɗanda suka fara tilastawa ƴan jam'iyyar sauya sheƙa.
Jaret Tenebe ya ce:
"APC ba ta da hannu a matsalolin da PDP ke fuskanta da ke sa ƴan jam'iyyar sauya sheƙa, nan da ƴan watanni wasu ƙarin ƴan siyasa za su shigo APC.
APC ta ja kunnen gwamnaan Ribas
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta gargaɗi gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya daina tsoma baki a harkokinta.
Cif Tony Okocha ne ya takawa gwamna burji biyo bayan hukuncin da bababr kotun Ribas ta yanke na tsige shugabannin APC a jihar Ribas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng