APC Ta Yi Babban Kamu, Jiga Jigan PDP Sun Koma Jam'iyyar, Sun Fadi Dalili
- Jam'iyyar APC ta ƙara samun tagomashi a jihar Imo bayan wasu jiga-jigan ƴan siyasa sun koma cikinta
- Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Imo, Chris Okewulonu, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar bayan ya yi murabus daga PDP
- Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya yi maraba da shigowarsu cikin APC inda ya bayyana cewa sun yanke shawara mai kyau
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Imo - Chris Okewulonu tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnati a lokacin tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya koma jam'iyyar APC.
Chris Okewulonu ya koma jam'iyyar APC ne tare da tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan Imo, Chuma Nnaji, wanda suka yi takara tare da Emeka Ihedioha.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta rahoto cewa mutanen biyu, tare da magoya bayansu, sun sauya sheƙa zuwa APC ne a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsofaffin Jiga-jigan PDP sun koma APC
Chris Okewulonu ya yi jawabi ga ƴan jam'iyyar APC a sakatariyarta da ke Owerri babban birnin jihar Imo.
"Za ku tuna cewa a ƴan watannin da suka gabata, na gabatar da takardar murabus a matsayina na mamba a jam’iyyar PDP, da kuma mamba a kwamitin amintattun ta."
"Na yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan na yi zurfin tunani, tare da doguwar tattaunawa da ƴan uwana, abokaina na siyasa da kuma masu goyon bayana."
- Chris Okewulonu
Tsohon jigon na PDP ya yaba da shugabancin Gwamna Hope Uzodimma da nasarorin da ya samu a jihar.
Gwamna Uzodimma ya yi musu maraba
Gwamna Hope Uzodimma ya yi maraba da dawowarsu zuwa jam'iyyar APC, yana mai jaddada cewa sun yanke shawara mai kyau.
"Ana kallon APC a matsayin baƙuwar jam’iyyar saboda rashin taɓuka abin kirki a baya. A yau jam’iyya ɗaya tilo da ta yi wa mutanen Imo aikin da ya dace ita ce APC."
- Gwamna Hope Uzodimma
Ya bayyana sauya sheƙar ta su a matsayin wata shaida da ke nuna ƙaruwar tasirin APC a jihar.
Ƴar majalisa ta caccaki PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ethiope daga jihar Delta, Eriathake Ibor-Suenu ta caccaki jam'iyyar.PDP.
Ƴar majalisar wacce ta sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ta bayyana cewa tsohuwarta jam'iyyarta ta mutu murus a mazaɓar Ethiope.
Asali: Legit.ng