Gwamna Ya Fito Ya Yi Magana kan Shirinsa na Neman Zama Shugaban Ƙasa a 2027
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi ƙarin haske kan raɗe-raɗin yana shirin fitowa takarar shugaban kasa a 2027
- A cewar gwamnan, yanzu ya maida hankali ne wajen kammala zangon mulki na biyu amma bai fara tunanin shugabancin kasa ba
- Makinde ya bukaci ɗaliban da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandire na jihar Oyo su cike fom na neman lamunin karatu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ba da amsar tambayar da ake yawan yi masa kan burin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa a halin yanzu ya maida hankali ne kan kammala wa'adin zango na biyu da al'ummar jihar Oyo suka ba shi amana.
Seyi Makinde ya yi wannan furucin ne a wata hira da manema labarai da safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, 2024 a Ibadan, babban birnin Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde zai nemi shugaban ƙasa?
Ya kara da cewa ya mayar da hankali ne wajen kammala wa’adinsa na biyu amma ko kaɗan bai fara tunanin tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027 ba.
Gwamnan ya ce:
“Ina da aikin da al’ummar Jihar Oyo suka ba ni, don haka shi ne abin da na fi mayar da hankali a kai a yanzu, ba shugabancin kasa a 2027 ba."
Yayin wannan tattaunawa da manema labarai, Makinde ya taɓo wasu ayyukan tituna da gwamnatinsa ke yi a faɗin jihar Oyo.
Ya yi wa al’ummar jihar Oyo alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala dukkan hanyoyin da ta fara ginawa ko take gyarawa.
Makinde ya kuma amsa rokon wani ɗalibi na rage kudin makaranta, inda ya roƙi dalibai su cike neman lamunin karatun gwamnatin tarayya.
Ku saurari ƙarin bayani...
Asali: Legit.ng