Babbar Kotu Ta Soke Matakin Majalisa, Ta Dawo da Ciyamomi 18 da Aka Dakatar
- Kotun jihar Edo mai zama a Benin ta dawo da dakatattun ciyamomi da mataimakansu na kananan hukumomi 18
- Wannan hukunci na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Majalisar dokoki ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin kan zargin almubazzaranci
- Alkalin kotun, mai shari’a Efe Ikponmwonba ya umarci kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa, ya ɗage zaman zuwa watan Fabrairu, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Babbar kotun Edo mai zama a Benin City ta soke matakin da majalisar dokokin jihar ta ɗauka kan shugabannin ƙananan hukumomi 18.
Idan baku manta ba Majalisar dokokin jihar Edo ta dakatar da ciyamomi 18 da mataimakansu a faɗin kananan hukumomin jihar kan zargin almubazzaranci.

Source: Twitter
Sai dai a zaman yau Juma'a, 20 ga watan Disamba, 2024 babbar kotun Edo ta soke wannan mataki na majalisa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta maido ciyamomi 18 kan kujerunsu
Kotun ta ba da umarnin maida dukkan ciyamomin da mataimakansu kan kujerunsu har zuwa lokacin da za ta gama sauraron karar kuma ta yi hukunci.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Efe Ikponmwonba ta ba da umarnin ne biyo bayan karar da ciyamomi da mataimakansu suka shigar gabanta.
Alkali ya takawa gwamnan Edo burki
Har ila yau umarnin kotun ya haka Gwamna Monday Okpebholo, gwamnatin Edo da sauran waɗanda ake tuhuma amfani da matsayar Majalisar dokoki.
Alkalin ya umarci kowane ɓangare su ci gaba da zama a yadda yake gabanin kotu ta gama da sauraron karar da aka shigar gabanta ranar 12 ga watan Disamba, 2024.
Daga nan ne alkalin mai shari’a Efe Ikponmwonba ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga Fabrairu, 2025, domin a ci gaba da sauraron ƙarar.
Bugu da ƙari, ya ba da umarnin a aika sammaci ga waɗanda ake tuhuma domin su san abin da ke faruwa kafin ranar zama na gaba.
EFCC ta gayyaci ciyamomin jihar Edo
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gayyaci shugabannin ƙananan hukumomin Edo zuwa ofishinta domin su amsa wasu tambayoyi.
A wata sanarwa da ta aikewa sakataren gwamnatin Edo, EFCC ta sanya wa ciyamomin ranakun da takon ganinau a ofishinta.
Asali: Legit.ng

