Ribas: Babbar Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar APC da 'Yan Kwamitin NWC

Ribas: Babbar Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar APC da 'Yan Kwamitin NWC

  • Babbar kotun Ribas ta tsige shugaban APC da sauran yan kwamitin gudanarwa na jihar waɗanda aka zaɓa kwanan nan
  • Mai shari'a Godswill Obomanu ya soke tarukan da aka zaɓi shugabannin APC na Ribas saboda take umarnin da ya bayar tun farko
  • Tsagin APC karkashin shugabancin Emeka Beke ne suka shigar da ƙara a gaban kotu, inda suka kalubalanci nasarar Tony Okocha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Wata babbar kotun Ribas mai zama a Fatakwal ta soke tarukan zaɓen shugabannin jam'iyyar APC na jihar.

Kotun ta rushe zaɓukan da APC ta gudanar wanda Cif Tony Okocha ya samu nasarar zama shugaban jam'iyyar reshen Ribas.

Tony Okocha.
Kotu ta soke zabukan shugabannin Jam'iyyar APC a jihar Rivers Hoto: Chief Tony Okocha
Source: Facebook

Dalilin soke tarukan APC a Ribas

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa babbar kotun ta soke tarukan ne saboda raina umarnin da ta bayar a baya na dakatar da tarukan.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya yi zazzaga, ya tona yadda aka rugurguza Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsagin APC karƙashin jagorancin Emeka Beke ne ya shigar ƙorafi a gaban kotun, ya nemi a soke zaɓen Okocha a matsayin shugaban jam'iyya.

Tun farko dai babbar kotun ta umarci APC ta dakatar da shirin da take na gudanar da tarukan da za a zaɓi shugabanninta a jihar Ribas.

Amma maimakon bin wannan umarni, jam'iyyar APC ta shure hukuncin kotun kana ta shirya tarukan kamar yadda ta tsara.

Jam'iyyar APC ta raina kotu a jihar Ribas

Wannan ya sa waɗanda suka shigar da ƙara suka sake komawa kotu, inda suka sanar da ita cewa APC ta shirya tarukan duk da umarnin da ta bayar.

Mai shari’a Godswill Obomanu na babbar kotun Ribas, bayan ya saurari bahasi daga bangarorin biyu, ya soke tarukan nan take, rahoton Daily Trust.

Hukuncin kotun na nufin tsige Tony Okocha daga matsayin shugaban APC a Ribas tare da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa (NWC).

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

APC ta dakatar da shugabanta na Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa APC ta dakatar da shugabanta na jihar Ondo, Ade Adetimehin, kan zarge-zargen da suka shafi rashin ɗa'a.

Shugabannin jam'iyya na gundumar Ofosu a ƙaramar hukumar Idanre ne suka ɗauki wannan matakin amma kakakin APC na Ondo ya ce ba za ta saɓu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262