'Mu Yaransa ne': Gwamnan PDP Ya Fadi yadda Jonathan Ya Rusa Masa Siyasarsa

'Mu Yaransa ne': Gwamnan PDP Ya Fadi yadda Jonathan Ya Rusa Masa Siyasarsa

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya bayyana yadda tafiyar siyasarsa ta kasance ƙarƙashin Goodluck Jonathan
  • Gwamnan ya ce tsarin tsohon shugaban ya taba masa siyasa kafin ya zama ɗan Majalisar Tarayya a shekarar 2015
  • Diri ya fadi irin tasirin da matakin Jonathan ya yi a siyasarsa a jihar Bayelsa da yadda hakan ya zamo masa alheri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya bayyana yadda shirin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya shafe shi siyasa.

Gwamna Diri ya ce lamarin ya shafi siyasarsa kafin tafiyarsa zuwa Majalisar Dattawa a birnin Tarayya, Abuja.

Gwamna ya bayyana yadda matakin Jonathan ya yi tasiri a siyasarsa
Gwamna Douye Diri ya fadi alakarsa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Hoto: Diri Douye, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Diri ya fadi tafiyar siyasarsa karkashin Jonathan

Diri ya fadi haka ne a bikin tunawa da marigayiya Madam Ani-Gunn Rhoda Ikiogha, mahaifiyar tsohon shugaban ma’aikata na gidan gwamnati, Diekivie Ikiogha cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya roƙi tsohon ɗan takarar gwamna ya koma jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce, a ƙarshe, shawarar tsohon shugaban kasar ta sauya burinsa na siyasa da kuma zama alheri a gare shi.

Diri ya ce shi da Ikiogha sun kasance yaran Jonathan a siyasa kafin ya zama shugaban kasa, suna aiki tare har sai da ra’ayinsu na siyasa ya saba.

“Na shafe lokaci mai tsawo tare da Chief Ikiogha, mun yi aiki tare a wani lokaci mai tsawo amma wata rana ya bar ni saboda ra’ayoyinmu sun bambanta, muna da abin da muke so."

- Diri Douye

'Yadda tsarin Jonathan ya shafi siyasa ta' - Gwamna Diri

Lokacin shugabarmu yana Abuja a matsayin shugaban kasa, don haka muka tsara makomar siyasarmu tare da tsohon gwamna, Sanata Dickson wanda ya kasance shugaban mu a nan."

“Muka yarda ni zan shiga Majalisar Dattawa, Chief Ikiogha kuma Majalisar Wakilai, har mun siya takardar tsayawa takara, amma mun san cewa abin da Jonathan ke so zai yi tsari."

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

“A ƙarshe, tsohon shugaban kasa ya zo da na shi tsari wanda ya shafe mu gaba ɗaya, wannan ne ya kawo rarrabuwar kawunanmu da Chief Ikiogha, kuma wannan ne karo na farko da muka rabu."

- Douye Diri

Gwamnan ya ce hakan ya zama alheri a gare shi saboda shi ne ya ba shi damar zama ɗan Majalisar Wakilai a 2015, cewar The Nation.

Gwamna ya koka kan rashin wutar lantarki

Kun ji cewa Gwamna Douye Diri ya koka kan lalacewar wutar lantarki tsawon watanni uku a jihar Bayelsa saboda katsewar wasu na'u'rorin TCN.

Diri ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tare da kamfanin samar da wuta na ƙasa watau TCN domin gyara matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.