Gwamna da Wasu Kusoshi Sun Sake Taso da Batun Tsige Shugaban PDP Na Ƙasa

Gwamna da Wasu Kusoshi Sun Sake Taso da Batun Tsige Shugaban PDP Na Ƙasa

  • Masu ruwa da tsakin PDP daga Arewa ta Tsakiya sun buƙaci shugabannin jam'iyya su ba yankin damar ƙarisa wa'adin Iyorchia Ayu
  • Sun ɗauki wannan matsaya ne a wani zama da suka yi a birnin tarayya Abuja wanda gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya halarta
  • Duk wani kokari na shirya taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC da ake tsammanin sauya Damagum ya ci tura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Manyan jagororin jam'iyyar PDP na Arewa ta Tsakiya sun gudanar da taro a Abuja kan batun kujerar shugabancin jam'iyya.

Sun jaddada cewa suna nan kan bakarsu ta neman a ba su damar karisa wa'adin tsohon shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya.

Umar Damagum.
Jiga-Jigan APC na Arewa ta Tsakiya sun jaddada bukatar dawo da kujerar shugaban jam'iyyar yankinsu Hoto: Umar Damagum
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun da aka tunɓuke Ayu, Ambasada Umar Damagum ya maye gurbin a matsayin miƙaddashin shugaban PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Batun tsige shugaban PDP ya dawo

Duk kokarin da ake na kiran taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ake sa ran kawo wanda zai maye gurbin Damagum ya ci tura.

A taron da suka yi a Abuja, masu ruwa da tsakin Arewa ta Tsakiya sun yi kira ga shugabannin PDP na sauran shiyyoyin da su mara wa yankin baya.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang, da tsaffin shugabannin majalisar dattawa, David Mark da Bukola Saraki, cewar Leadership.

Arewa ta Tsakiya ta ci gaba da fafutuka

Sanarwar da suka fitar bayan taron ta ce:

"Muna da yakinin PDP na bin kundin tsarin mulkinta a koda yaushe, saboda haka ya kamata shugabannin jam'iyya su tashi tsaye wajen haɗa kan mambobi."
"Ya zama dole masu ruwa da tsaki su cika yarjejeniya ta hanyar bai wa Arewa maso Tsakiya damar cika wa'adinta."

Sun kuma tabbatar da cewa PDP a Arewa ta tsakiya a dunƙule take kuma ta shirya jan ragamar jam'iyyar zuwa matakin nasara.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani a PDP, an kori mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa

PDP ta caccaki kasafin kuɗin 2025

A wani rahoton, an ji cewa jam'iyyar PDP ta caccaki kasafin kuɗin 2025 da shugaban ƙasa, Bola Ahmeɗ Tinubu ya gabatar ranar Laraba.

Babbar jam'iyyar adawa ta kasa ta bukaci Majalisa ta yi amfanin ƙarfin ikonta wajen sauya kasafin ya dawo kan hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262