Ganduje: An Fara Samun Ɓaraka a Jam'iyyar APC Reshen Jihar Kano? Gwarzo Ya Yi Bayani
- Ibrahim Ɗan'azumi Gwarzo ya musanta raɗe-raɗin cewa ɓaraka ta kunno kai a jam'iyyar APC reshen jihar Kano
- Babban jigon ya ce kasuwar APC zuwa gidan siyasa daban-daban ba zai zama abin damuwa ba matukar aka haɗa kai a zaɓe da tarukan jam'iyya
- An dai fara raɗe-raɗin cewa Barau ya kafa gidan siyasarsa, haka Ganduje da Gawuna/Garo, lamarin da ya sa ake ganin APC ta rabu gida-gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wani babban jigon APC a Kano, Ibrahim Dan’azumi Gwarzo, ya musanta batun cewa an samu baraka a cikin jam’iyyar.
Ya ce rikicin cikin gida da ake zargin ya ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Kano ba gaskiya ba ne, kansu a haɗe yake wuri guda.
Ibrahim Gwarzo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust kan abubuwan da ke faruwa a APC yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta rabu gida-gida a Kano?
Ya ce rarrabuwar APC zuwa gida-gida a Kano ba wani abin damuwa ba ne domin zai kara mata ƙarfi kuma ba zai ruguza shirin da jam'iyyar ke yi ba.
Ibrahim.Ɗan'azumi ya ce:
"Rabuwa zuwa tawaga-tawaga, ra'ayoyi ko abin da kuke kira gida-gida na siyasa ba wata matsala ba ce matukar za mu haɗa kai a batun zaɓe ko tararrukam jam'iyya.
"Ku tuna fa APC ce ke mulkin ƙasa, ita ce jam'iyyar da ke mulki a jihohi 19 kuma an yi hasashen daga nan zuwa 2027 za su karu zuwa jihohi 30.
"Saboda haka ina ganin wannan karkasuwa zuwa gida-gida na da alaƙa da girman jam'iyyar, matukar kowa zai bi doka bana tunanin za a samu matsala.
Da sanin Ganduje Barau ke jawo ƴan NNPP
Ibrahim Gwarzo ya ƙara da cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya fara jawo ƴan NNPP zuwa APC ne da izinin shugaban jam'iyya, Abdullahi Ganduje.
Ya yi wannan furucin ne domin musanta raɗe-raɗin cewa APC a Kano ta dare gida-gida, kama daga gidan Barau, Ganduje da kuma Gawuna/Garo.
Abdullahi Abbas ya ba ƴan APC shawara
Rahoto ya gabata cewa shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bukaci ƴaƴan APC su haɗa kansu domin cimma nasara a zaɓe na gaba.
Abdullahi Abbas ya bayyana cewa haɗin kan cikin gida shi babban makamin da ya kamata APC ta fara mallaka gabanin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng