Bayan Gano Ma'aikatan Bogi, Gwamna Namadi Ya Kori Hadimarsa da Suke Yanki Daya

Bayan Gano Ma'aikatan Bogi, Gwamna Namadi Ya Kori Hadimarsa da Suke Yanki Daya

  • Gwamna Umar A. Namadi na jihar Jigawa ya fatattaki wata daga cikin hadiminsa a yau Laraba 18 ga watan Disambar 2024
  • Gwamna ya amince da korar haridmarsa a bangaren jinsi, Khadijah Sidi Sulaiman daga mukaminta
  • Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ya fitar da yammacin yau Laraba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya kori hadimarsa ta musamman a bangaren jinsi.

Gwamna Namadi ya amince da sallamar Khadija Sidi Suleiman daga mukaminta ba tare da bata lokaci ba.

Gwamna Namadi ya fatattaki hadimarsa daga muƙaminta
Gwamna Umar Namadi ya kori daya daga cikin hadimansa, Khadijah Sidi Sulaiman daga mukaminta. Hoto: Umar A. Namadi.
Asali: Twitter

Gwamna Namadi ya sallami hadimarsa a Jigawa

Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Tinubu ya gwangwaje Kwankwaso, Bichi da manyan mukamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Bala Ibrahim ya ce Gwamna Namadi ya fatattaki Khadija Sidi Sulaiman daga mukaminta a bangaren jinsi a jihar.

“Gwamna Malam Umar A. Namadi ya sauke Khadija Sidi Suleiman daga mukaminta na hadima ta musamman a bangaren jinsi nan take.”

- Bala Ibrahim

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an soke dukkan hakkoki da fa’idodin da suka shafi ofishinta.

Umarnin da Gwamna Namadi ya ba Khadija

An umarci Khadija Sidi Suleiman da ta mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunta kai tsaye ga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Jigawa.

Duk da cewa sanarwar ba ta bayyana dalilin sallamar ta ba, ta nuna godiya ga hidimomin da ta bayar a jihar tare da yi mata fatan alheri a rayuwarta ta gaba.

Tsohuwar hadimar wacce 'yar asalin garin Kafin Hausa ce, inda Gwamna Namadi ya fito ita ce hadima ta biyu da aka sallama a cikin watanni uku.

Gwamna Namadi ya bankado ma'aikatan bogi

Kara karanta wannan

Sanata Abdul Ningi ya buga muhawara da Akpabio a majalisar dattawa

Kun ji cewa Gwamnatin Jigawa tana cigaba da aikin tantance ma'aikatan jihar domin gano na bogi masu karɓar albashi ba bisa ƙa'ida ba.

A aikin tantancewar, gwamnatin Jigawa ta bankaɗo ma'aikatan bogi guda 6,348 da ke samun kuɗaɗe ba tare da gudanar da aiki ba.

Kwamishinan yaɗa labarai, matasa da wasanni na jihar Jigawa, Sagir Musa ya ce gwamnatin ta rage kashe N3.6bn a shekara sakamakon gano ma'aikatan na bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.