A ƙarshe, Tinubu Ya Gwangwaje Ilyasu Kwankwaso, Bichi da Manyan Mukamai
- Hon. Musa Ilyasu Kwankwaso ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu a yau Laraba 18 ga watan Disambar 2024
- Tinubu ya amince da nadin Ilyasu Kwankwaso da Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi a hukumar raya kogunan Hadejia-Jama’are
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman, Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa a yau Laraba 18 ga watan Disambar 2024.
Tinubu ya amince da nadin sababbin shugabanni a hukumomin raya kogunan da ke karkashin ma’aikatar Ruwa ta Tarayyar Najeriya.
Tinubu ya ba Musa Ilyasu Kwankwaso mukami
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na Facebook a yau Laraba 18 Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce an nada Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, Daraktan Gudanarwar Kuɗi a Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are da ke kula da Kano, Jigawa da Bauchi.
Daga cikin sababbin nade-naden, an tabbatar da Injiniya, Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayin Babban Darakta na hukumar.
Ga cikakken jerin sunayen waɗanda aka nada:
Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are (Kano, Jigawa da Bauchi)
1. Mamman Da’u Aliyu – Shugaban Hukuma (Jigawa)
2. Engr. Rabiu Suleiman Bichi – Babban Darakta (Kano)
3. Tijjani Musa Isa – Daraktan Gudanarwa, Shirye-shirye da Tsarawa (Jigawa)
4. Hajiya Zainab Gamawa – Daraktar Gudanarwa, Ayyukan Noma (Bauchi)
5. Baffa Dandatti Abdulkadir – Daraktan Gudanarwa, Injiniya (Kano)
6. Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso – Daraktan Gudanarwa, Kuɗi (Kano).
Tinubu ya ba Bwala Daniel muƙami
Mun ba ku labarin cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ba tsohon hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar mukami a gwamnatinsa.
Mr. Daniel Bwala ya samu muƙamin ne a gwamnatin Bola Tinubu a ranar Alhamis 14 ga watan Nuwambar 2024 bayan ya dawo jam'iyyar APC.
Tinubu ya amince da nadin Bwala a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa da hulda da jama'a.
Asali: Legit.ng