Rikici Ya Ƙara Tsanani a PDP, An Kori Mataimakin Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa

Rikici Ya Ƙara Tsanani a PDP, An Kori Mataimakin Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa

  • Rikicin PDP ya ƙara tsananta yayin da aka kori mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa mai kula da shiyyar Kudu maso Gabas, Cif Ali Odefa
  • Shugabannin PDP a matakin gumdumarsa da ke jihar Ebonyi ne suka kore shi bayan dakatarwar da aka masa a watan Satumba, 2024
  • Sun bayyana cewa sun kori Odefa daga PDP ne bisa shawarwarin kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Rigingimun cikin gida na ci gaba da dagulawa jam'iyyar PDP lisssafi tun bayan kammala babban zaɓen 2023.

A halin yanzu dai PDP a gundumar Oguduokwor da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi ta kori mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Chief Ali Odefa.

Shugaban PDP, Umar Damagum.
PDP ta kori mataimakin shugaban jam'iyya na Shiyyar Kudu maso Gabas Hoto: Umar Damagum
Asali: Twitter

Yadda rikicin PDP a gundumar ya faro

Vanguard ta tattaro cewa a ranar 11 ga watan Satumba, 2024, shugabannin PDP na gundumar suka dakatar da Odefa bisa zargin cin amanar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Sanata Abdul Ningi ya buga muhawara da Akpabio a majalisar dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka babbar kotun tarayya mai zama a Abakaliki ta tabbatar da dakatar da shi a ranar 29 ga Nuwamba, 2024 a kara mai lamba FHC/AI/CS/182/2024.

Yanzu kuma shugabannin PDP na gunduma a Ebonyi sun kori mataimakin shugaban jam'iyya mai kula da shiyyar Kudu maso Gabas, Cif Ali Odefa.

Shugaban PDP na gundumar, Hon. Onyeka Herbert Ovuta tare da abokan aikinsa ne suka sanar da korar jigon a yayin zantawa da manema labarai ranar Laraba.

Dalilin korar mataimakin shugaban PDP

Ya ce sun ɗauki matakin ne bayan karɓan shawarin kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar PDP, rahoton Premium Times.

Ovuta ya ce:

"Korar Cif Ali Odefa ta biyo bayan rahoto, bincike, da shawarwarin kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar, wanda ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin PDP.”
"Sakamakon dakatarwa da kuma korarsa da aka yi yanzu, daga yau Cif Ali Odefa ba shi da alaƙa da PDP"

Wannan matakin dai shi ne na karshe da shugabannin PDP suka ɗauka kan Odefa a matakin gunduma bayan zarginsa da cin amanar jam'iyya.

Kara karanta wannan

Ana neman Obasanjo, IBB, Buhari, Jonathan su hadu, su kifar da Tinubu a 2027

Tsohon minista ya fice daga PDP

A wani labarin kun ji cewa tsohon minista a Najeriya, Bolaji Abdullahi ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP.

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa sai da ya yi tunani mai zurfi kafin ɗaukarmatakin barin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262