Abin da Ƴan APC Za Su Yi a Kano domin Karɓe Mulki daga Hannun Abba a 2027
- Abdullahi Abbas ya yi kira da ƴaƴan APC A Dawakin Kudu da Warawa su haɗa kansu wuri guda domin shirya tunkarar zaɓen 2027
- Shugaban APC reshen Kano ya ce haɗin kai shi ne babban makamin jam'iyyar wanda zai ba ta damar ƙwato mulki daga hannun NNPP a jihar
- Ya yi wannan furuci ne a wurin bikin karɓar dubban ƴan NNPP da suka jefar da tafiyar Kwankwasiyya, suka dawo APC a Dawakin Kudu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi kira ga ɗaukacin ƴaƴan jam'iyyar su dunkule su haɗa kai wuri ɗaya gabanin zaɓen 2027.
Abdullahi Abbas ya bayyana cewa haɗin kai shi ne babban makamin da zai ba APC damar kwato mulkin Kano daga hannun jam'iyyar NNPP.
APC na shirin tunkarar zaɓen 2027
Shugaban jam'iyyar ya yi wannan furuci ne a wurin taron karɓan dubban ƴaƴan NNPP da suka sauya sheka zuwa APC a Dawakin Kudu/Warawa, Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren APC na Kano, Malam Ibrahim Sarina ne ya karɓi masu sauya sheƙar a madadin Abdullahi Abbas a wani taro da aka shirya a garin Dawakin Kudu.
Abin da zai taimaki APC a zaɓen Kano
“Ina kira ga dukkan magoya bayanmu da wadanda suka shigo cikinmu a yau da su hada kai mu tabbatar mun shirya tunkarar zaben 2027.
"Muna kira ga daukacin 'yan jam'iyyar APC musamman na Dawakin Kudu da Warawa da mu hada kai mu kasance masu rikon amana, mu guji fadace-fadacen cikin gida, mu zama tsintsiya ɗaya."
“Wannan yana da matukar muhimmanci, ya kamata ’yan APC na wannan mazabar su rungumi juna, su yafe dukkan abin da ya faru a baya, a ɓirne baya a tunkari gaba."
- In ji Abdullahi Abbas.
Shugaban jam'iyyar APC ya jaddada cewa haɗin kai shi ne ƙashin bayan duk wata nasara da jam'iyyar ke fatan samu a zaɓuka masu zuwa, rahoton Daily Post.
Jigon APC ya buƙaci Kawu Sumaila ya baro NNPP
Rahoto ya gabata cewa AbdulMajeed Danbilki Kwamanda ya yi kira ga Sanata Kawu Sumaila ya daina wano rabe-raɓe, ya shigo jam'iyyar APC.
Sai dai jigon APC ya ja hankalin Sanata Kawu ya guji sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu idan har yana son cimma burinsa a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng