"Zai Lalubo Hanya," Ministan Tinubu Ya Bayyana Gwamnan da Zai Dawo APC
- Festus Keyamo ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti zai dawo jam'iyyar APC nan ba da jimawa ba
- Ministan sufurin jiragen sama ya misalta zaman Otti a LP da ɗan da ya ɓata a hanya wanda daga baya zai nemo gida
- Alex Otti ya zauna a APC a shekarar 2020 bayan ya baro APGA, sai dai daga bisani ya koma LP kuma ya lashe zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kwatanta zaman gwamnan Abia, Alex Otti a LP da yaron da ya ɓata wanda daga bisani zai nemo hanyar komawa gida.
Alex Otti dai ya zauna a jam'iyyar APC a 2020 bayan ya baro APGA, amma daga bisani ya sauya sheƙa zuwa LP kuma ya samu nasarar zama gwamna a 2023.
Keyamo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da ginin filin jirgin sama na jihar Abia, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu na son Gwamna Otti a APC
Ministan ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu yana son gwamnan Abia kuma ya faɗa masa kalamai masu daɗi game da shi.
Festus Keyamo ya ce:
"Shugaban ƙasa na da ƙwarin guiwa a kan gwamna kuma hakan alama ce da ke nuna yana son shi. Na san kalaman da ya faɗa kan gwamnan Abia da yadda al'umma ke kaunarsa."
"Yau ba ranar siyasa ba ce, amma ku sani da yana tare da mu sai kuma ya kauce kamar dai ɗan da ya yi ɓatan hanya."
Za a gina babban filin jirgin sama a Abia
Ministan ya kara da cewa an ɗaga darajar filin jirgin ya zama na ƙasa da ƙasa maimakon manufar farko ta gina filin cikin gida kawai.
"Lokacin da na kira Alex Otti na faɗa masa filin ƙasa da ƙasa za a gina, cewa ya yi zai haɗa kai da mu, kuma zai kara jawo wasu takwarorinsa a aiki," in ji shi.
Gwamma Otti ya maido ilimi kyauta a Abia
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alex Otti ya maida ilimin firamare da na sakandire kyauta a jigar Abia da ke Kudu maso Gabas.
Kwamishinan sadarwa na Abia ya ce wanna mataki na ilimi kyauta zai kawo karshen koke-koken iyaye na rashin kudin da za su sa ƴaƴansu makaranta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng