Majalisar Ta Dakatar da Shugabannin Ƙananan Hukumomi 18 da Mataimakansu
- Majalisar dokokin Edo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar bisa zargin almubazzaranci da rashin ɗa'a
- Wannan mataki ya biyo bayan wasiƙar da Gwamna Okpebholo ya aika majalisar, yana mai cewa ciyamomin sun ƙi kawo masa rahoton kudi
- Bayan zazzafar mahawara a zaman yau Talata, majalisar ta dakatar da ciyamomi da mataimakansu a faɗin kananan hukumomin Edo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Majalisar dokokin jihar Edo a ranar Talata, ta dakatar da dukkan zababbun shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakansu.
Majalisar ta ce ta dakatar da ciyamomin da nataimakinsu a faɗin kananan hukumomi 18 na jihar Edo bisa zargin almubarrazanci da kudi da rashin ɗa'a.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Majalisar ta dauki matakin ne a zaman yau Talata, 17 ga watan Disamba, 2024 bayan zazzafar muhawara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma umarci shugabannim majalisun kowace ƙaramar hukuma su karɓi ragamar tafiyar da harkokin gwamnati daga nan zuwa watanni biyu masu zuwa.
Yadda majalisa ta dakatar da ciyamomi 18
Dakatar da ciyamomin da mataimakansu ya biyo bayan kudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa maso Gabas, Hon. Isibor Adeh ya gabatar
Hon. Donald Okogbe, memba mai wakiltar mazabar Akoko-Edo II ya goyi bayan kudirin nan take.
Tun farko dai Gwamna Okpebholo ya aika wasiƙa ga Majalisar, inda ya sanar da ita cewa ciyamomi sun ƙi miƙa rahoton kuɗi ga gwamnatin jihar Edo.
Dalilin dakatar da shugabannin hananan hukumomi
Gwamnan ya bayyana abin da ciyamomin suka yi na yin fatali da umarninsa a matsayin rashin ladabi da biyayya, ya bukaci majalisar ta duba lamarin.
Yayin muhawara kan kudirin dakatar da ciyamomin, ƴan majalisa 14 sun goyi baya, shida kuma suka ƙi yarda, yayin da uku suka tsaya a tsakiya, rahoton Daily Trust.
Gwamnan Edo ya rusa hukumomin gwamnati
Rahoto ya gabata cewa Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya. rusa hukumomin gwamnati tare da korar shugabanninsu nan take.
Sakataren gwamnatin Edo ya ce gwamnan ya umarci dukkan shugabannin hukumomin su mika kayan gwamnati da ke hannunsu ga babban jami'in da ke wurin.
Asali: Legit.ng