"Za Mu Kwace Mulki a 2027," APC da Ganduje Sun Kara Rikirkita Jam'iyyar NNPP a Kano

"Za Mu Kwace Mulki a 2027," APC da Ganduje Sun Kara Rikirkita Jam'iyyar NNPP a Kano

  • Jam'iyyar APC da Abdullahi Ganduje sun ƙara rikita NNPP mai mulkin Kano a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027
  • Ƴaƴan NNPP sama da 2,000 a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a hukumance
  • Sakataren APC na Kano, Malam Ibrahim Zakari Sirina ya ce wannan alama ce da ke nuna jam'iyyar za ta ƙwato mulkin Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Akalla ƴa ƴan jam'iyyar NNPP 2,000 ne suka watsar da tafiyar Kwankwasiyya, suka koma APC a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Kano.

Masu sauya shekar sun tabbatar da komawa inuwar jam'iyyar APC ne a wani taro da aka shirya domin tarbarsu a karamar hukumar Dawakin Kudu.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar NNPP a Kano ta kara rasa dubannin mambobinta a Dawakin Kudu Hoto: OfficialAPCNG
Source: Twitter

APC na shirin kwace mulkin Kano a 2027

Da yake jawabi a wurin, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya ce wannan wata alama ce da ke nuna jam'iyyar za ta ƙwace mulki a 2027, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Baraka a NNPP: Kawu Sumaila ya fadi dalilin alakarsa da jam'iyyar APC

Sakataren jam'iyyar, Malam Ibrahim Zakari Sarina, wanda ya wakilci Abdullahi Abbas, ya ce tururuwar ƴan NNPP zuwa APC na nuna inda Kano ta dosa a zaɓe na gaba.

Yadda APC ta karɓi dubannin ƴan NNPP

Malam Ibrahim Zakari ya ce:

"Ku ƙara hakuri, mun san ba ku jin daɗin yanayin yadda ake tafiyar da al'amura da harkokin mulkin jihar Kano."
"A yanzu da kuka dawo jam'iyyarmu muna tabbatar maku da cewa da mu da ku mun zama ɗaya, daman mafi yawanku duk ƴaƴan APC ne.
"Yanzu kun samu damar ganin banbancin jam'iyar mu da ta su, muna maku maraba da dawowa APC, mun zama ɗaya."

Dalilin canza shekar ƴan NNPP zuwa APC

Da yake magana a madadin wadanda suka sauya sheka, Sulaiman Dalibi ya bayyana cewa shi da ƴan NNPP 2,000 sun koma inuwar APC.

"A yau kuma a yanzu, ni da wadannan ƴan NNPP sama da 2,000 mun koma APC. Za mu ci gaba da gwagwarmayar samar da ingantacciyar Kano a karkashin tsarin dimokuradiyya mai adalci.”

Kara karanta wannan

2027: Ana kukan mulkinsu, Ganduje ya ce zai kwace jihar da APC ba ta taɓa mulki ba

Sai dai wani ɗan Kwannwasiyya ya bayyana cewa duk waɗannan masu sauya sheƙar ba ƴan NNPP ba ne tun asali.

Malam Abdullahi Sa'idu ya shaidawa Legit Hausa cewa babu wani ɗan Kwankwasiyya akida da zai iya barin gidan Kwankwaso.

"Duk wani ɗan Kwankwasiya da kaga ya barta to dama zuwa ya yi, ban cire ma kowa hula ba. Kuma zancen APC na shirin kwace mulki ga fili ga mai doki, mu haɗu a akwatun zaɓen a 2027," in ji shi.

2027: Tinubu ya samu goyon baya a Arewa

A wani labarin kun ji cewa ƴaƴan APC a Arewa ta Tsakiya sun bayyana cewa za su sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Shugaban kungiyar APC a shiryyar, Saleh Zazzaga ya ce tun da damokuraɗiyya ta dawo, babu shugaban da ya zuba masu aiki kamar Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262