Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutane 8 a Muhimmam Muƙamai

Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutane 8 a Muhimmam Muƙamai

  • Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa manyan sakatarori takwas a gwamnatin tarayya ranar Litinin, 16 ga Disamba
  • Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa
  • Shugaba Tinubu ya roki waɗanda ya naɗa su maida hankali, himma da ƙwazo wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin manyan sakatarorin guda takwas a gwamnatin tarayya domin cike gurbin da ake da su.

Wannan shi ne rukuni na biyu na manyan sakatarori takwas da shugaban kasa ya naɗa, bayan waɗanda ya amince da naɗinsu a watan Yuni, 2024.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Bola Tinubu ya amince da nadin manyan sakatarori 8 a gwamnati Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya naɗa manyan sakatarori

Mai baa shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Atiku ya buɗe shafin da yan Najeriya za su samu tallafin N65,000? Hadiminsa ya yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ne ya ba da shawarin waɗanda ya cancanta a naɗa a muƙaman.

Hadimin shugaban ƙasar ya kuma hero sunayen sababbin manyan sakatarorin da jihohin da suka fito a Najeriya.

Jerin sunayen sabbabin sakatarori da jihohinsu

1. Onwusoro Maduka Ihemelandu (Jihar Abia)

2. Ndiomu Ebiogeh Philip (Jihar Bayelsa)

3. Anuma Ogbonnaya Nlia (Jihar Ebonyi)

4. Ogbodo Chinasa Nnam (Jihar Enugu)

5. Danjuma Usman (Jihar Gombe)

6. Usman Salihu Aminu (Jihar Kebbi)

7. Oyekunle Patience Nwakuso (Jihar Rivers)

8. Nadungu Gagare (Jihar Kaduna)

Shugaban ƙasa Tinubu ya bukaci sababbin manyan sakatarorin da su nuna himma, kwazo da nemo sababbin hanyoyin zamani wajen yi wa kasa hidima.

Bola Tinubu ya canza ranar gabatar da kasafi

A wani rahoton, an ji cewa Shugaba Tinubu ya sauya tunani game da shirinsa na gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a ranar Talata, 17 ga watan Disamba 2024.

An ruwaito daga Majalisar tarayya cewa mai grima shugaban ƙasa ya ɗage ranar gabatar da kasafin saboda wasu dalilai da suka sha ƙarfimsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262