'Yadda aka yi wa Buhari Dabaibayi, aka Hana Shi Sakat a Shekaru 8,' Dalung
- Tsohon ministan tarayya, Solomon Dalung ya ya yi zargin cewa 'yan ba-ni-na-iya sun karɓe ikon mulki bayan nasarar Buhari a 2015
- Barista Solomon Dalung ya ce waɗanda suka yi yaƙin neman zaɓen Muhammadu a 2015 Buhari sun rasa damar yin tasiri a mulkinsa
- Dalung ya bayyana cewa a yanzu jam’iyyar APC ta shiga cikin rudani da wani irin yanayi ba kamar lokacin da aka kafa ta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuaj, Nigeria - Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi zargin cewa wasu 'yan-ba-ni-na-iya sun karɓe ragamar mulki bayan nasarar da Muhammadu Buhari ya samu a 2015.
Solomon Dalung bayyana cewa an naɗa wasu mutane domin su taimakawa shugaban ƙasa amma suka jagoranci mulkinsa bisa son zuciyarsu.
Punch ta wallafa cewa Solomon Dalungya yi maganganun ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Lahadi da ta wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya faru bayan Buhari ya lashe zabe?
Solomon Dalung ya yi ikirarin cewa bayan Buhari ya lashe zaɓe a shekarar 2015, wasu mutane da ba a san da su ba suka fara ware waɗanda suka yi yaƙin neman zaɓensa gefe.
"Lokacin da aka bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓe, na kasance tare da shi a ofishinsa.
Na je ganin sa da yamma a wannan ranar. Sai dai kuma, an hana ni shiga gidan sa, alhali a daren da ya gabata har ƙarfe 2 dare ina tare da shi.”
- Solomon Dalung
Dalung ya ce sai bayan ya kira wasu mutane aka ba shi damar shiga, kuma daga wannan lokacin ne 'yan-ba-ni-na-iya suka karɓe iko da mulkin shugaba Buhari.
An iy wa Buhari dabaibayi inji Dalung
Daily Trust ta rahoto cewa tsohon ministan ya zargin cewa waɗanda suka yi aiki tukuru domin ganin Buhari ya ci zaɓe ba su samu wata dama a gwamnatin ba.
Ya ce tunda 'yan-ba-ni-na-iya suka karɓe ikon mulkin suka rika jagorancin gwamnatin Buhari bisa muradun kansu har tsawon shekaru takwas.
Solomon Dalung ya ce a yanzu haka lamuran APC sun rikice ba kamar yadda aka yi fafutukar kafa ta a baya ba.
APC ta yi martani ga Kwankwaso da Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani bayan Sanata Rabi'u Kwankwaso da Donald Duke sun ziyarci Olusegun Obasanjo.
Jam'iyyar APC ta ce hadaka ko taron 'yan adawa ba zai daga mata hankali ba kasancewar Bola Tinubu yana daidai da kowane dan siyasa a kasar nan.
Asali: Legit.ng