PDP Ta Samu Koma Baya, Tsohon Minista Ya Fice daga Jam'iyyar, Ya Fadi Dalilinsa
- Tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa a Najeriya, Bolaji Abdullahi, ya raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa a Kwara
- Bolaji Abdullahi ya sanar da yin murabus daga PDP inda ya ce ya ɗauki matakin bayan ya ɗauki lokaci yana tunani
- Tsohon ministan wanda ya yi takarar sanata a zaɓen 2023 ya bayyana cewa bai gama yanke shawara kan jam'iyyar da zai koma ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, Bolaji Abdullahi, ya yi murabus daga jam’iyyar PDP.
Tsohon ministan ya sanar da ficewarsa ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Disamba, wacce ya ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Ubandawaki a jihar Kwara.
Bolaji Abdullahi ya yi murabus daga PDP
Jaridar The Cable ta ce Bolaji Abdullahi ya tabbatar mata da ficewarsa daga PDP a ranar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya kuma ce har yanzu bai yanke shawarar jam'iyyar da zai tattara komatsansa ya koma ba.
Ya bayyana cewa ya bar komai a hannun Allah kan mataki na gaba da zai ɗauka na komawa wata jam'iyyar siyasa.
Meyasa ya tsohon ministan ya fice daga PDP?
A cikin wasiƙar murabus ɗin, Bolaji Abdullahi ya ce ya cimma matakin ne mai tsauri bayan ya kwashe kwanaki yana nazari da tunani.
Ya nuna godiyarsa ga shugabannin PDP kan damar da suka ba shi ta yin aiki tare da jam'iyyar.
"Na rubuto ne domin na yi murabus daga jam'iyyar PDP a hukumance."
"Na samu isasshen lokacin yin tunani, kuma na cimma matsaya mai wahala kan cewa wannan shine kawai zaɓin da zan iya ɗauka a wannan lokacin."
- Bolaji Abdullahi
Bolaji Abdullahi ya kasance ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen sanatan Kwara ta tsakiya a shekarar 2023. Ya sha kaye a hannun Salihu Mustapha na jam’iyyar APC.
Ƴar majalisar PDP ta koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ethriatake Ibori-Suenu mai wakiltar mazaɓar Ethiope a majalisar wakilai ta sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Ƴar majalusar wacce ɗiyar tsohon gwamnan Delta ce, ta sauya sheƙar ne a zauren majalisa a ranar Alhamis, 5 ga watan Disamban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng