Bayan Cika Bakin Ganduje, An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC

Bayan Cika Bakin Ganduje, An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC

  • Shugabannin APC a matakin gundumar Ofosu cikin ƙaramar hukumar Idanre sun dakatar da shugaban APC na jihar Ondo
  • An dakatar da Ade Adetimehin ne bisa zargin rashin ɗa'a da kuma yin wasu kalamai waɗanda za su iya tayar da tarzoma
  • Sai dai, daraktan yaɗa labaran APC na jihar Ondo, ya yi fatali da dakatarwar wacce ya bayyana a matsayin ba ta inganta ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Shugabannin jam'iyyar APC na gundumar Ofosu a ƙaramar hukumar Idanre, sun dakatar da shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin.

Shugabannin na APC sun dakatar da Ade Adetimehin ne bisa zargin rashin ɗa’a da kuma fitar da wasu kalamai da ka iya haifar da rikici.

APC ta dakatar da shugabanta na Ondo
An dakatar da shugaban APC na jihar Ondo Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

An dakatar da shugaban APC a Ondo

Tashar Channels tv ta ce takardar dakatarwar tana ɗauke da sa hannun shugaban APC na gundumar Ofosu, Olabisi Adepegba.

Kara karanta wannan

Bayan ba Jonathan damar takara, 'yan adawa sun fara sabon shirin hadaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran masu hannu a takardar sune shugabanni 14 da suka haɗa da mataimakin shugaba, Olabisi Oyewole da sakatare, Olanrewaju Akinnuoye.

Dakatarwar na zuwa ne bayan wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a sakatariyar APC ta jihar, inda suka buƙaci Adetimehin da ya yi murabus.

APC ta yi kumfar baki kan dakatar da shugabanta

Sai dai, daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihar Ondo, Steve Otaloro, a wata sanarwa da ya fitar game da lamarin ya yi watsi da buƙatar Adetimehin ya yi murabus.

Otaloro ya kuma bayyana cewa ba a bi hanyoyin da suka dace ba wajen dakatarwar, inda ya bayyana ta a matsayin wacce ba ta inganta ba.

Daraktan yaɗa labaran ya dage cewa har yanzu Adetimehin ne shugaban jam’iyyar APC a jihar Ondo.

"Hukuncin da shugabannin APC na gundumar Ofosu a ƙaramar hukumar Idanre suka yanke, bai dace da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar mu ba, domin haka ba shi da amfani."

Kara karanta wannan

Batutuwa 30 sun jawo taron ECOWAS a Najeriya, ministoci sun hallara a Abuja

"Dalilan da aka ambata na wannan dakatarwar ba su da inganci, wanda ke nuna cewa an yi hakan ne saboda wani dalili na ƙashin kai ba damuwa game da shugabanci ba."
"Muna son nanata cewa Ade Adetimehin har yanzu shi ne shugaban jam'iyyar APC na jihar Ondo."

- Steve Otaloro

Ganduje ya cika baki kan jihar Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci rantsar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin APC na jihar Rivers.

Ganduje a wajen taron rantsar da shugabannin, ya cika bakin cewa jihar Rivers ce ta gaba da jam'iyyar za ta ƙwace a 2027, bayan ta yi nasara a zaɓen gwamnan Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng