Gwamna a Arewa Ya Sauya Sheƙa daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC? Gaskiya Ta Fito
- Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Mutfwang ya yi Allah wadai da wani hoto da ke yawo cewa an gan shi tare da gwamnonin APC kuma wai suna jiran Bola Tinubu
- Ya ce duk wannan wani makirci ne na wasu masu son tada fitina da ɗauke hankalin jama'a daga biyayyarsa ga jam'iyyar PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Gwamnan jihar Filato, Caleb Nutfwang ya sake karyata raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya gama shirin sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
A ƴan kwanakin nan jita-jita ta ƙara tashi musamman a kafafen sada zumunta cewa gwamnan ya raba gari da jam'iyyar PDP, ya koma APC.
Gwamna Mutfwang ya koma jam'iyyar APC?
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an daɗe ana alaƙanta Gwamna Mutfwang da shirin komawa APC, inda a kwanan nan batun ya sake yaɗuwa a soshiyal midiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma Gwamna Mutfwang ya sake fitowa ya ƙaryata labarin, yana mai cewa wasu bara gurbi ne suka kirkiro jita-jitar da nufin haɗa shi faɗa da PDP.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gwamnan Filato, Gyang Bere ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis, 12 ga Disamba, Daily Trust ta kawo.
Gwamnan Filato ya yi Allah wadai da rahoton
"Gwamna Caleb Mutfwang, ya musanta jita-jitar da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa ya sauya sheka zuwa APC.
"Mutfwang ya alaƙanta jita-jitar da aikin wasu masu ɓarna da ke kokarin raba kawuna da yaudarar jama'a game da tsantsar biyayyar da yake wa PDP.
"Gwamnan ya kuma yi Allah-wadai da rahoton da ake yadawa, wanda ke nuna hotonsa na karya tare da gwamnonin APC, inda aka ce wai suna shirin tarbar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Edo.
- in ji Gyang Bere.
Ana shirin warware rikicin jam'iyyar PDP
Gwamna Mutfwanga ya kara da cewa duk an kirkiri wannan karyar ne domin ɗauke hankulan jama'a da kuma sa masu shakku kan biyayyar da yake yi wa PDP.
Ya kuma tabbatar wa ‘ya’yan PDP na Filato da shiyyar Arewa ta tsakiya cewa suna ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar.
Ɗan LP a Filato ya sauya sheka zuwa APC
Rahoto ya gabata cewa wani dan Majalisar Tarayya daga jihar Plateau ya sake komawa APC a ranar Alhamis 12 ga watan Disambar 2024.
Ɗan Majalisar mai suna Ajang Iliya ya watsar da jam'iyyar LP ne domin ba yan mazabarsa wakilci nagari a jihar Plateau.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng