Rigima Ta Barke a Majalisar Tarayya da 'Dan LP daga Arewa Ya Koma Jam'iyyar APC
- Wani dan Majalisar Tarayya daga jihar Plateau ya sake komawa jam'iyyar APC a yau Alhamis 12 ga watan Disambar 2024
- Dan Majalisar mai suna Ajang Iliya ya watsar da jam'iyyar LP ne domin ba yan mazabarsa wakilci nagari a jihar Plateau
- Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar LP ta rasa akalla mambobi shida da suka sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rigima ta barke a Majalisar Tarayya yayin da dan jam'iyyar LP ya koma APC mai mulkin Najeriya.
'Dan Majalisar, Ajang Iliya da ke wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas ya sauya sheka zuwa APC.
An kai ruwa rana a Majalisar Tarayya
The Nation ta ce mambobin Majalisar daga ɓangaren adawa sun ki amincewa da sauya shekar inda suka ta da bore.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin Majalisar sun bukaci a ayyana kujerar dan Majalisar babu kowa saboda saba ka'ida da ya yi.
Dawowar dan Majalisar zuwa APC ya zama na shida daga cikin mambobin Majalisar da suka sauya sheka.
'Dan Majalisa daga LP ya koma APC
Yayin da take karanta wasikar sauya shekar, shugaban Majalisar, Tajudden Abbas ya ce Iliya ya bar LP ne saboda rikicin jam'iyyar.
Hon. Abbas ya ce dan Majalisar ya kuma dawo APC saboda ayyukan alheri da Bola Tinubu ke yi a Najeriya, cewar rahoton Punch.
Dan Majalisar ya ce ya koma APC ne saboda ba yan mazabarsa wakilci nagari wanda hakan zai fi sauki idan yana jam'iyya mai mulki.
Yar Majalisa da ta koma APC ta rasa kujerarta
Kun ji cewa Jam'iyyar PDP ta ayyana kujerar Hon. Erhiatake Ibori-Suenu babu kowa bayan ta koma APC mai mulkin Najeriya.
Jam'iyyar ta dauki matakin ne kan yar tsohon gwamnan Delta, James Ibori domin hukumar INEC ta sake gudanar da wani zabe.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da Erhiatake ta fitar da take sanar da ficewarta daga PDP saboda rikice-rikice a jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinyewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng