'Yana da Kwarin Guiwa a 2027'; An Fadi Shirin da Tinubu Ya Yi game da Zabe

'Yana da Kwarin Guiwa a 2027'; An Fadi Shirin da Tinubu Ya Yi game da Zabe

  • Hadimin Bola Tinubu na musamman, Daniel Bwala ya koka kan yadda wasu ke kwatanta Najeriya da kasar Ghana
  • Bwala ya ce ƙasashen kwata-kwata tsarinsu ba iri daya ba ne duba da yanayin cigaba da siyasarsu a halin yanzu
  • Wannan martani na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa zaben Ghana zai yi matukar tasiri a shekarar 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hadimin Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake surutu a kai.

Daniel Bwala ya musanta rade-radin cewa zaben kasar Ghana zai yi tasiri a na Najeriya a shekarar 2027.

Hadimin Tinubu ya yi alfahari kan zaben 2027 a Najeriya
Daniel Bwala ya ce Bola Tinubu yana da kwarin guiwa kan zaben 2027. Hoto: Bwala Daniel.
Asali: Twitter

Bwala ya fadi shirin Tinubu a zaben 2027

Bwala ya bayyana hakan ne a yau Laraba 11 ga watan Disambar 2024 a birnin Abuja yayin wata ziyarar da ya kai Hedikwatar jam’iyyar APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Bwala ya bayyana cewa shugaba Tinubu yana da kwarin gwiwa kan babban zaɓe mai zuwa a shekarar 2027.

Da aka tambaye shi ko fadar shugaban kasa tana cikin damuwa kan sakamakon zaben Ghana, Bwala ya ce yanayin ba iri ɗaya bane, Peoples Gazette ya ruwaito.

Bwala ya bambance Najeriya da kasar Ghana

“Idan aka yi nazari tsakanin kasashen, ba wai na caccaki gwamnatin Ghana ba ne, amma akwai bambance-bambance a cikin manufofin gwamnati."
“Idan kuna bibiyar al’amuran Ghana cikin shekara ɗaya da ta gabata, kuma kuka dubi alamu za ku gano cewa abin da ke faruwa a kasashen biyu ba iri ɗaya ba ne."
"Abin da shugaban kasa yake yi wajen sake daidaita tattalin arzikin Najeriya yana kan madaidaiciyar hanya, yana da matuƙar kwarin gwiwa."

- Bwala Daniel

An sauyawa Bwala muƙami a gwamnatin Tinubu

Kun ji cewa kwanaki kadan bayan nada Daniel Bwala a mukamin hadimin Bola Tinubu, an fayyace masa matsayinsa sabanin yadda yake nufi.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

Hadimi a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya ci gyaran Bwala bayan ayyana kansa a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa.

Onanuga ya ce an yi wasu sauye-sauye kan mukaman masu magana da yawun shugaban kasa inda ya ce sun kai mutum uku yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.