Gwamna na Kuntatawa 'Yan Majalisu Masoyan Tsohon Gwamna? Hadiminsa Ya Magantu
- Gwamnatin jihar Benue ga ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa tana nuna wariya ga wasu yan Majalisar dokoki
- Gwamna Hyacinth Alia shi ya karyata labarin ta bakin hadiminsa a bangaren sadarwa, Solomon Iorpev a jihar
- Wannan na zuwa ne bayan zargin gwamnan da hana wasu yan Majalisu hakkokinsu saboda biyayyarsu ga George Akume
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya yi martani kan rade-radin nuna wariya a Majalisar dokokin jihar.
Hyacinth Alia ya musanta rahoton da ke cewa yana wariya ga 'yan Majalisar dokoki da ake zargin masu biyayya ne ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Ana zargin Gwamna da kuntatawa 'yan Majalisu
Gwamnan ya bayyana hakan ta bakin hadiminsa, Solomon Iorpev yayin da yake mayar da martani kan rahoton, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin na zuwa ne bayan rahoton wata kungiya mai suna ‘Alliance for Good Governance’.
Kungiyar ta zargi gwamnan da hana wasu ‘yan Majalisar kudin tallafin mazabunsu da kuma motocin aiki.
Gwamnatin Benue ta mayar da martani kan jita-jitar
A cewar Iorpev, gwamnan da ‘yan Majalisar sun cimma matsaya kan wasu matsaloli da suka shafi sayen motocin aiki da batutuwan da ke damun mambobinsu.
Iorpev ya ce sabanin ikirarin kungiyar, gwamnan na tafiya tare da dukkan mambobin Majalisar dokoki ta jihar.
“Idan wani abu yana faruwa akwai dalili, kuma na tabbata ‘yan Majalisar ma sun fahimci hakan, wanda ya sa babu wanda ya nuna rashin jin dadi."
“Domin haka, idan wani daga waje ke magana meyasa suke kuka fiye da wadanda abin ya shafa? Gwamnan da ‘yan Majalisar sun cimma matsaya.”
- Solomon Iorpev
'Dan Majalisa ya goyi bayan kudirin haraji
Kun ji cewa dan Majalisar Tarayya daga yankin Arewacin Najeriya ya yabawa Bola Tinubu kan sabon kudirin haraji da ke gaban Majalisa.
Hon. Philip Agbese daga jihar Benue ya ce yan Najeriya za su yabawa Tinubu daga baya kan wannan kokarin da yake yi.
Agbese ya kuma yabawa hukumar tattara haraji ta FIRS kan irin sababbin dabarun samun kuɗi da take kawowa a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng