'Sarki 1 ne a Kano': Ado Doguwa Ya Soki Masu Cewa Jihar na da Sarakuna 2

'Sarki 1 ne a Kano': Ado Doguwa Ya Soki Masu Cewa Jihar na da Sarakuna 2

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nuna takaici kan yadda ake kwatanta Kano tana dauke da sarakuna biyu da kuma gwamnoni biyu
  • Ado Doguw mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa ya ce idan aka ce akwai gwamna biyu a Kano,bai zai yi musu ba amma Sarki daya ne
  • Hakan na zuwa ne yayin da sabuwar rigima ta barke da Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi shirin zuwa Bichi nadin hakimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi magana kan rigimar sarauta a masarautar Bichi.

Hon. AlhassanAdo Doguwa ya ce abin takaici ne yadda ake cewa a Kano akwai sarakuna biyu da kuma gwamnoni biyu.

Ado Doguwa ya yi magana kan rigimar sarauta a Kano
Hon. Ado Doguwa ya nuna takaici kan abin da ke faruwa na rigimar sarauta a Kano. Hoto: Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Asali: Twitter

Ado Doguwa ya koka kan rigimar sarautar Kano

'Dan Majalisar ya bayyana haka ne a wani bidiyo da shafin Hon. Alhassan Ado Doguwa TV ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Uwar bari: Lauya ta ba Bello El Rufai hakuri da ya yi barazanar maka ta a kotu kan kazafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ado Doguwa ya ce duk dan siyasa ba zai ji dadin a ce Kano na da sarakuna biyu da gwamnoni biyu ba.

Doguwa ya ce bai tsoron kowa kuma zai fada Sarkin Kano na gaskiya shi ne Aminu Ado Bayero.

Hon. Ado Doguwa ya fadi alhinin Sarki a Kano

"An wayi gari a ce akwai sarakuna biyu, wani lokacin ma a ce gwamnoni biyu a Kano, abin takaici ne shugaba nagari dole ya ji takaicin wannan abu."
"Idan aka ce gwamnoni biyu ne a Kano ba zan yi jayayya ba amma ban da maganar sarakuna biyu."
"Amma duk wanda ya ce sarakuna biyu ne a ina jin ranar zuwa bikin nadin sarauta a Bichi ya san waye Sarki."
"Duk dan jihar Kano ya san waye ne sarki kuma idan akwai mai bukatar fassara zan fada ba tare tsoron uban kowa ba Sarki Aminu Ado Bayero shi ne Sarki."

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

- Alhassan Ado Doguwa

Ado Doguwa ya nemi afuwar APC

A baya, kun ji cewa Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nemi yafiyar jam'iyyar APC a jihar Osun.

Hon. Doguwa ya ce an juya masa magana ne domin biyan buƙatar kansu ta siyasa inda ya ce APC ce za ta yi a zabe mai zuwa.

Hakan na zuwa ne bayan Hon. Ado Doguwa ya yabawa Gwamna Ademola Adeleke kan ayyukan alheri abin da ya batawa APC rai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.