'Har Acaba Na Yi a Da': Sanata Ya Tuno Rayuwar da Ya Yi a Shekarun Baya

'Har Acaba Na Yi a Da': Sanata Ya Tuno Rayuwar da Ya Yi a Shekarun Baya

  • Sanata a Najeriya ya bayyana irin gwagwarmayar da ya yi a rayuwa kafin zama ɗan Majalisar Tarayya
  • David Jimkuta ya ce har aikin acaba ya yi a rayuwarsa domin rufawa kansa asiri kafin shiga Majalisa a yau
  • David Jimkuta da ke wakiltar Taraba ta Kudu ya yabawa salon jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata David Jimkuta daga jihar Taraba ya magantu kan wahalar rayuwa kafin shiga Majalisar Tarayya.

Sanata David Jimkuta da ke wakiktar Taraba ta Kudu ya bayyana yadda ya yi aikin acaba a baya a rayuwarsa.

Sanata y bayyana irin wahalar da ya sha a rayuwarsa
Sanata David Jimkuta ya ce har acaba ya yi domin dogaro da kai. Hoto: Senator David Jimkuta.
Asali: Facebook

Sanata ya fadi wahalar da ya sha a rayuwarsa

Sanata Jimkuta ya bayyana haka ne a bidiyo yayin wani taro a Abuja da Channels TV ta wallafa a yau Talata 10 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

'Gidan yari ya sauya ni' Hon. Farouk Lawan ya magantu, ya yabawa siyasar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya yabawa Ministan Abuja, Nyesom Wike kan irin himmatuwarsa wurin gudanar da ayyuka a Abuja.

Daga bisani, ya yabawa salon shugabancin Sanata Godswill Akpabio saboda himmatuwarsa wajen cigaban Najeriya.

"Ina jin dadin abin da kake yi, saboda kafin na zama Sanata na taba yin aikin acaba.
"Kuma na ba wasu babura domin tallafa musu a matsayina na dan siyasa bayan na shiga Majalisa."
"Abin da kake yi abin a yaba ne mai girma Minista hakan da kake yi kana karawa yan yankinka kwarin guiwa ne."

- David Jimkuta

Sanata Jimkuta ya kora yabo ga Nyesom Wike

Sanatan daga bisani ya ce za su cigaba da ba Wike goyon baya domin gudanar da ayyukan alheri.

Dan Majalisar ya ce Wike yana karawa takwarorinsa karfin guiwa domin kara musu kaimi wurin ayyukan alheri.

Tsohon Sanata ya koka da wahalar rayuwa

A baya, kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari a bangaren siyasa ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan Faransa, gwamnatin Tinubu ta kulla sabuwar yarjejeniya da kasar Pakistan

Tsohon sanatan jihar Ekiti, Babafemi Ojudu ya ce har fitsari ya sha a gidan yari domin ya rayu a zamanin sojoji.

Sanata Ojudu ya kuma tuno yadda aka cafke shi sau fiye da 15 a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha saboda gwagwarmaya da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.