Dattawan Arewa Sun Soki Kalaman Sakataren Gwamnati kan Takara da Tinubu a 2027

Dattawan Arewa Sun Soki Kalaman Sakataren Gwamnati kan Takara da Tinubu a 2027

  • Kungiyar 'Arewa Consultative Forum' ta fusata da kalaman da sakataren gwamnati, George Akume ya yi kan zaben 2027
  • Jami'in yada labaran ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba ya ce dacewa ya yi gwamnati ta mayar da hankali a kan ci gaba
  • Sakataren gwamnatin tarayya ya shaida cewa ba su fitar da matsaya a kan wanda za su zaba a kakar zabe mai kamawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa ta ACF ta soki fadar shugaban ƙasa kan cewa shugaba Bola Tinubu zai ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2031.

Kungiyar ta shawarci Bola Ahmed Tinubu a kan abin da ya dace ya yi, a maimakon mayar da hankali a kan zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

Tinubu
ACF ta caccaki lamirin dan Arewa kar ya tsaya zaben 2027 ba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce bai dace a fata muharar zaben 2027 tun yanzu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarar ACF ga Gwamnatin Bola Tinubu

Kungiyar ACF ta shawarci gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali ga bijiro da samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan kasa.

Wannan na zuwa bayan kalaman sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na cewa bai dace Arewa ta sa rai da sake darewa mulkin shugabancin kasar nan bas ai bayan 2027.

Matsayar dattawan Arewa a kan zaben 2027

Dattawan Arewa sun bayyana ba za ta ɗauki matsaya na siyasa ba kan wanda za a zaɓa ko wanda za a ƙi zaɓa ba a 2027.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ACF, Muhammad Baba ya ce abin da ke gabansu a yanzu shi ne jin dadin al’umar da su ka yi zabe a kasar.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji da abubuwa 9 da suka yi wa gwamnatin Tinubu illa a Arewacin Najeriya

ACF ta dakatar da shugabanta saboda sukar Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar ACF ta dakatar da shugabanta na kasa, Mamman Mike Osuman bisa kalaman da ya yi na cewa ba za su zabi Bola Tinubu a 2027 ba.

Shugaban, wanda ya fusata a kalaman da ya yi a kan salon mulkin Tinubu ya bayyana cewa tsare-tsaren da aka zo da su, sun takura jama'a tare da jefa rayuwarsu a mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.