Zaɓen Ghana: Saraki Ya Fadi Darasin da INEC da Majalisa Za Su Koya a Najeriya
- Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya yabawa hukumar zaben kasar Ghana
- Saraki ya ce zaben da aka gudanar a ranar Asabar darasi ne ga hukumar INEC a Najeriya da Majalisar Tarayya
- Tsohon gwamnan Kwara ya ce ya kamata hukumar INEC ta inganta yadda take gudanar da zabe wurin amfani da fasaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara - Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki ya magantu kan zaben kasar Ghana da aka gudanar.
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya ce zaben da aka gudanar a Ghana ya kamata ya zama darasi ga hukumar INEC da Majalisa.
Bukola Saraki magantu kan zaben Ghana
Saraki ya fadi haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin 9 ga watan Disambar 2024, cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya yi kira ga hukumar INEC da ta kawar da kowanne dalili na gudanar da zaɓe ta hanyar gargajiya domin inganta harkokin zabe.
Sanaran ya bukaci a ƙarfafa matakan da za su hana ko rage yuwuwar maguɗin zaɓe domin murɗa sakamakon.
Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan zaɓen Ghana, Saraki ya ce hakan wani gargaɗi ne ga INEC da Majalisar Ƙasa kan buƙatar sake nazarin tsarin zaɓe don ya zama mai inganci.
Bukola Saraki ya ba hukumar INEC shawara
Saraki ya ce kafin Najeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta a matsayin jagorar Afirka, akwai buƙatar INEC ta rungumi amfani da fasaha domin inganta tsarin zaɓe.
"Yanayi irin na yadda aka gudanar da zaɓen Ghana a ranar Asabar, 'yan takara suka san sakamakon da zai sanya jam'iyya mai mulki ta amince da shan kaye, ba zai yiwu ba sai da ingantacciyar fasaha."
Saraki ya yi watsi da hujjar da ke cewa Ghana karamar kasa ce idan aka kwatanta da Najeriya.
"Ko da lokacin da INEC ke gudanar da zaɓe a jiha guda, ba a fitar da sakamako cikin hanzari yadda za a san shi safiyar da ta biyo bayan zaɓe kamar yadda aka yi a Ghana ba."
- Bukola Saraki
Mahmood Yakubu ya yabawa hukumar zaben Ghana
Kun ji cewa shugaban hukumar INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya yabawa kasar Ghana kan yadda aka gudanar da zabe.
Farfesa Yakubu ya koka kan yadda yan siyasar da ake da su a Najeriya ke sauya sheka lokacin da suka ga dama ba kamar Ghana ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng