An Yi Musayar Yawu da Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sanar da Komawa APC
- Jam'iyyar LP ta kara yin babban rashi, ɗan Majalisar wakilai daga jihar Filato, Hon Dalyop Chollom ya sauya sheƙa zuwa APC
- Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar da Chollom ya aiko a zaman ranar Talata, 10 ga watan Disambar 2024
- Sai dai sauya shekar da haddasa musayar yawu tsakanin Tajudeen Abbas da shugaban marasa rinjaye, Hon. Kingsley Chinda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani ɗan jam'iyyar LP a Majalisar wakilan tarayya, Hon. Dalyop Chollom ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki da rinjaye.
Ɗan Majalisar mai wakiltar Barkin Ladi/Riyom a jihar Filato, ya sanar da barin LP tare da komawa APC ne a zauren Majalisar wakilai da ke Abuja.
Kakakin Majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ne ya sanar da sauya sheƙar Hon. Chollom a wata wasiƙa da ya karanta a zaman yau Talata, Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin sauya sheƙar ɗan Majalisar LP
Ɗan majalisar ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsallakawa zuwa APC bayan ya yi tunani kuma bisa dalilin rigingimun da suka dabaibaye jam'iyyar LP.
Dalyop Chollom ya ƙara da cewa makomar siyasar mutanen mazaɓarsa ta fara tangal-tangal a inuwar LP shiyasa ya yanke shawarar komawa jam'iyya mai mulki.
Sai dai shugaban marasa rinjaye, Hon. Kingsley Chinda (PDP, Rivers) ya yi fatali da sauya shekar, inda ya kafa hujja da sashe na 68 (1) (d) na kundin tsarin mulki.
Bisa haka ya roki Majalisar wakilai ka da ta amince da wasikar sauya sheƙar Hon Chollom, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
An yi musayar yawu a Majalisar Wakilai
Hon. Chinda ya kara da cewa ya kamata dan majalisar ya bayar da hujjar ficewa daga LP, amma Tajudeen Abbas ya ce ya ga komai kuma ya gamsu da abin da Chollom ya gabatar.
Duk da haka shugaban marasa rinjaye ya ƙara maida martani da cewa idan kakakin majalisa ya gamsu, to ya zama dole ya ayyana kujerar Chillom a matsayin babu kowa.
Tajudeen ya maida masa raddi da cewa ya karanta dukkan abin da ɗan majalisar ya gabatar a wasiƙarsa, don haka koken shugaban marasa rinjaye bai karɓu ba.
Hakazalika, dan majalisar wakilai, George Ozodinobi (Anambra, LP) ya ce sauya shekar abin takaici ne saboda babu wani rikici da ke faruwa a jam’iyyar LP.
Ƴan majalisa 4 na LP sun koma APC
Ku na da labarin ƴan majalisar wakilai guda huɗu da aka zaba a inuwar jam'iyyar LP a zaɓen 2023 sun tattara kayansu sun koma APC mai mulki.
Ƴan majalisun sun sanar da haka ne a zaman Majalisa na ranar 5 ga watan Nuwamba, sun ce rigimar shugabanci ta hana jam'iyyar LP motsi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng